Zaɓen Amurka: Ruɗanin da Amurka ke fuskanta ya janyo tsoro da fargaba

Trump ya fice daga dakin da ya yi wannan jawabi yayin wani taro a fadar White House da ke Washington DC, USA, a ranar 04 ga watan Nuwamba 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin lashe zaɓen kasar da misalin karfe 2:30 na daren ƙasar
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Cikin sama da makonni, Donald Trump ya ta nanata cewa da an ƙare zaɓen shugabancin ƙasar, zai shigar da abokin takararsa na jam'iyyar Democrat ƙara game da maguɗin zaɓe da kuma yunkurin karɓe nasarar da ya yi.

A safiyar ranar Laraba sai ya yi hakan, lokacin da ya rage miliyoyin kuri'u da ba a ƙirga ba, sai ya yi ikirarin samun nasara a zaben.

"Mun shirya tsaf domin lashe wannan zaɓe, babu ɓoye-ɓoye, mun lashe wannan zaɓe," kamar yadda ya yi ikrari.

Ba tare da gabatar da wata hujja ba, ya ci gaba da yaɗa cewa an yi "magudi" a zaben.

"Wannan shi ne babban maguɗin da aka taɓa yi a tarihin ƙasar mu. Muna so a yi amfani da shari'a ta yadda ya kamata. Dan haka zamu garzaya kotun ƙoli. Muna buƙatar a dakata da ƙirga kuri'un da aka kaɗa."

Abin takaici, 'Abin da ba a yi tsammani ba, abin da ba daidai ba'

Dan takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Democrat Joe Biden tare da matarsa Jill, ya na gabatar da jawabi bayan sakamakon farko da aka samu na zaɓen shugabancin ƙasar daga jihohin Wilmington, Delaware a ranar 04 ga watn Nuwamba 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Joe Biden ya ce ' ba a kammala zaɓe ba har sai an ƙirga duka ƙuri'un da aka kaɗa'

Cikin gaggawa wasu 'yan jam'iyyar Democrat sun mayar da martani.

Abokin hamayyar Trump na jam'iyyar Democrat, Joe Biden ya ce zaɓen bai ƙare ba "har sai an kammala kirga ƙuri'un da aka kaɗa".

"Muna kan tafarkin nasara," in ji Biden.

Shugabar yaƙin neman zaɓen Biden, Jen O'Malley Dillion ta ce ikirarin Trump "abin takaici ne, abin da ba a yi tsammani ba ne, kuma ba daidai ba ne".

"Abin takaici ne saboda hakanƙoƙarin take 'yancin mutan Amurka ne a dimokradiyyance," ta ƙara da cewa.

"Abu ne da ba a yi tsammani ba saboda ko a tarihin ƙasarmu ba a taɓa shugaban da ya yi ƙoƙarin danne muryar 'yan Amurka a yayin zaɓen ƙasar."

Wata 'yar jam'iyyar dimokrat Alexandria Ocasio-Cortez, wadda aka sake zaɓa a matsayin 'yar majalisa, ta yi Allah wadai da ikirarin Trump a matsayin "Abin da ya saɓawa shari'a, mai cike da haɗari da ya yi kama da kama-karya".

Ta wallafa a shifinta na Twitter cewa " A ƙirga kuri'u. Sannan a mutunta sakamakon zaɓe,".

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ko 'yan jam'iyyar Republican da Trump ya ke, kamar su tsohon sanata daga jihar Pennsylvania Rick Santorum, ya nuna damuwa kan wannan batu.

Santorum ya ce, kalaman Trump sun matuƙar ɓata masa rai. "Amafani da kalmar maguɗi.... Ina ganin kuskure ne," kamar yadda ya shaida wa CNN.

Haka Ben Shapiro, wani mai sharhi kuma mai yawan sukar Trump ya wallafa a Twitter cewa, wannan "kalaman babu tunani a cikinsu".

Bayan Trump ya gama bayaninsa mataimakinsa Mike Pence ya so ya yi wa zancen kwaskwarima, yana cewa duk halattacciyar kuri'ar da aka kaɗa za a tabbatar da an kirga ta.

'An riga an yi katoɓara'

Masu aikin zabe na kirga kuri'un zaben 2020 na Amurka a Philadelphia a Pennsylvania ranar 3 ga watan Nuwamba 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Akwai kuri'u da dama da aka kaɗa ta email da har yanzu ba a gama kirgawa ba a Pennsylvania, daya daga cikin jihohi masu mahimmanci a zaben

An riga an gama yin katoɓara, in ji wakilin BBC a arewacin Amurka, Anthony Zurcher.

"Ko Trump ya lashe zaben bisa ka'ida ko kuma ya sha kaye, ya riga ya haifar da shakku kan zaben," in ji Zurcher.

Wannan matsalar annobar korona ya haifar da abin da ba a yi zato ba, saboda 'yan Amurka da dama sun yi zaɓe ta intanet ne, wanda hakan janyo bukatar karin lokaci domin kirga kuri'un.

A wasu jihohin zai ɗauki kwanaki kan kammala ƙirgen.

Anthony Zurcher ya ce "zaben Amurka na cikin wani ruɗani da ya haifar da firgici a zukatan Amurkawa, yayin da shugaban kasar ke ikirarin rashin amincewa da kuri'un da aka kaɗa - daga fadar White House".

Cikin ɗagawa Trump ya ce ba zai karɓi faduwa ba a zaben da ake yi.

A makonnin da suka gabata, wannan ya janyo wata muhawara kan ko za a kira sojoji ne ko kuma 'yan sanda somin fitar da shugaban daga White House idan ya fadi.

Rashin tabbas

An ta kafe hotuna a jikin katangar wayan da ke kofar shiga White House a ranar 2 ga watan Oktoba 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An sanya wata katangar waya mai matukar tsaro a wajen fadar White House kwanaki gabanin zaben

Yanzu tseren shugabancin ƙasar na ƙara takaituwa zuwa wasu jihohi da ba su fi a kirga ba, da suka hadar da Arizona da Navada da Pennsylvania da kuma Georgia.

Duk wani ƙalubalen da zai ta so sai an fara garzayawa kotun jiha da farko, in kuma ya yi karfi sai a tsallaka kotun koli. Wanda hakan ke nuna cewa da yi yuwar zai dauki kwanaki kan a sanar da shi.

A gefe daya kuma akwai tsoron cewa za a iya fuskantar tarzoma da sunanan zanga-zanga.

Ko a lokacin da zaben ya matso an ta fuskantar gutsiri tsoma da kuma rikice-rikice a zanga-zangar da aka yi a wasu bangarorin kasar da dama, ciki har da gaban White House.

"Wanne irin rintsi Amurka ke neman faɗawa, lokacin da Biden ke cewa suna kan turbar nasara shi kuma Trump na kukan an yi magudi ana kuma kokarin kwace nasararsa," in ji Zurcher.