'Yan bindiga sun kashe mutum 70 a yankin Tillaberi na jamhuriyar Nijar

Niger

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Duk da cewa babu wata kungiya da ta dauki alhakin wadannan nan hare-hare, jami'ai a kasar sun zargi kungiyoyi masu ikrarin jihadi daga iyaka da kasar Mali.

A baya dai an sha kai hare-hare yankin na Tillaberi al'amarin da ya sa aka sanya wa yankin dokar ta-baci tun 2017.

Ko a watan Mayun bara ma sai da wasu 'yan bindiga haye a Babura suka kasha mutum akalla 20 a wasu kauyuka.

Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke shirin shiga zango na biyu na zaben shugaban kasa.

Abin da hakan ke nufi shi ne duk dan takarar da ya yi nasara to zai gaji dimbin matsalar tsaro daga shugaban mai barin gado, Mahamadou Issoufou.

Kuma matsalar tsaron ba wai ta takaita ne bag a iyakar kasar da Mali, kudu maso gabashin kasar ma na da nata matsalar tsaron.

Ko a watan Disamban 2020 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hare-hare a yankin Diffa inda suka kashe mutum 27.

Ƙungiyar ta kuma ƙone ɗaruruwan gidaje da kasuwa da motoci a harin da ta kai da ta shafe sa'a uku a a ƙauyen Toumour a tsakanin daren Asabar zuwa Lahadi.

Mutane da dama ne aka ƙone bayan cinna wa gidajensu wuta, kuma da dama sun ɓata sun shiga daji.

An kai harin ne yayin da ƙasar ke shirin zaɓen ƙananan hukumomi a ranar Lahadi.

Bayanai sun ce tsakanin gida 800 zuwa 1,000 aka ƙone. Mayakan sun kuma kashe mutane bayan buɗe masu wuta.