Coronavirus a Amurka: Cutar Korona ta kashe mutum 3,900 cikin awa 24 a Amurka

An wallafa

Mutum fiye da 3900 ne suka mutu a Amurka a cikin awa 24. Jami'ar John Hopkins Universty ta Amurka mai taskace bayanan annobar a Amurkar ce ta wallafa bayanin.

Jihar California ta kasance ta biyu a kasar da ta samun masu dauke da sabon nau'in annobar mai saurin kisa.

A watan Satumbar 2020 ne dai aka gano sabon nau'in cutar a Kudu maso gabashin Burtaniya.

Dama dai kafin wannan nau'in cutar mai saurin bazuwa da kisa, Amurkar ce kan gaba wajen yawan wadanda annobar ta kashe a fadin duniya, inda ta dauki kaso daya bisa uku na yawan matattu.

Shugaba Trump ya sa hannu a makare kan wani gagarumin shirin tallafin rage raɗaɗin annobar korona da kuma ƙudurin dokar kashe kuɗi ta gwamnati zuwa doka.

Shi dai, tun da farjo ya ce ya fi son Amurkawa su samu wani babban ɗunƙulen tallafi a ɗaiɗaikunsu, kuma a cire agajin ƙasashen waje.

'Yan majalisa daga jam'iyyar Dimokrat da takwarorinsu na Rifablikan sun yi ta roƙonsa don ya sa hannu kafin ƙarewar wa'adin wani kasafin kuɗi a tsakar daren jiya.

Majalisar Wakilai ce ta amince da ƙunshin tallafin na dala biliyan 900 bayan an kwashe tsawon watanni ana tattaunawa.

Kuɗin wani ɓangare ne na ƙunshin dala tirliyan2.3 da ke ƙunshe da kasafin kuɗin wasu hukumomin gwamnatin tarayya na yau da kullum.

Miliyoyin Amurkawa da ke faɗi-tashi saboda annobar korona ne suka rasa samun agajin da akan bai wa marasa aikin yi na wani ɗan lokaci da kuma ƙarin kuɗaɗen gaggawa saboda jinkirin da aka samu.