Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: Birtaniya za ta fara amfani da riga-kafin cutar na biyu
Hukumomi a Birtaniya sun amince a fara yi wa mutane riga-kafin cutar korona wanda Jami'ar Oxford da kamfanin AstraZeneca suka samar.
Samun riga-kafin zai taimaka wurin dawo da rayuwa kamar yadda aka saba a ƙasar.
Sakataren Harkokin Lafiya Matt Hancock ya ce za a fara raba ta ranar 4 ga watan Janairu "kuma za a hanzarta da zarar an shiga makonnin farko na sabuwar shekara".
Birtaniya ta yi odar miliyan 100 na riga-kafin wanda kamfanin AstraZeneca ya samar - kuma zai isa a yi wa mutum miliyan 50.
Amincewar da hukumar kula da ingancin magunguna ta yi na fara amfani da shi na nufin riga-kafin ba shi da wata illa.
Riga-kafin Oxford-AstraZeneca, an fara samar da shi ne tun a watannin farko na shekarar 2020.
An fara gwada shi a kan mutum na farko a watan Afrilu kafin daga baya a gwada shi a kan ɗaruruwan mutane.