Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Korona: Trump ya sa hannu kan tallafin korona na $900bn
Shugaba Trump ya sa hannu a makare kan wani gagarumin shirin tallafin rage raɗaɗin annobar korona da kuma ƙudurin dokar kashe kuɗi ta gwamnati zuwa doka.
Shi dai, tun da farjo ya ce ya fi son Amurkawa su samu wani babban ɗunƙulen tallafi a ɗaiɗaikunsu, kuma a cire agajin ƙasashen waje.
'Yan majalisa daga jam'iyyar Dimokrat da takwarorinsu na Rifablikan sun yi ta roƙonsa don ya sa hannu kafin ƙarewar wa'adin wani kasafin kuɗi a tsakar daren jiya.
Majalisar Wakilai ce ta amince da ƙunshin tallafin na dala biliyan 900 bayan an kwashe tsawon watanni ana tattaunawa.
Kuɗin wani ɓangare ne na ƙunshin dala tirliyan2.3 da ke ƙunshe da kasafin kuɗin wasu hukumomin gwamnatin tarayya na yau da kullum.
Miliyoyin Amurkawa da ke faɗi-tashi saboda annobar korona ne suka rasa samun agajin da akan bai wa marasa aikin yi na wani ɗan lokaci da kuma ƙarin kuɗaɗen gaggawa saboda jinkirin da aka samu.
Da wa'adin ya ƙare, sai dai wasu hukumomin gwamnati su rufe ayyukansu, sai dai fa idan 'yan majalisa ne suka kaɗa ƙuri'a da rinjayen kashi biyu cikin uku.
Shugaba Trump ya ƙi amincewa da wasu ɓangarorin ƙudurin dokar duk da yake, da Sakataren Baitulmalinsa aka yi tattaunawar.
Shugaba Trump wanda har yanzu ke jin haushin faɗuwar zaɓen da ya yi, ƙememe ya bijirewa matsin lamba daga jam'iyyun biyu.
Waklliyar BBC ta ce daidai lokacin da yake buga ƙwallon gwaf, miliyoyin Amurkawa a yanzu sun rasa damar samun tallafin tsawon wani ɗan lokaci, kuma suna fuskantar barazanar korarsu daga gidajen haya.
Babu dai masaniya a nan kusa kan dalilin da ya sa Mista Trump - wanda ke jihar Florida - a ƙarshe ya yanke shawarar sa hannu a kan ƙudurin dokar.
Wani ɗan majalisar dattijai daga jam'iyyar Rifablikan Pat Toomey ya ce shugaban ya yi sa'a, da an riƙa tuna shi da kawo "hargitsi da ƙunci da kuma halin rashin mutunci".
Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden ya yi gargaɗi kan "mummunan sakamako" idan Mista Trump ya ci gaba da jinkirin sa hannu da ƙudurin dokar.