Muhammadu Buhari: 'Tsoron me ya sa Majalisa ta janye gayyata?'

Asalin hoton, SENATOR SHEHU SANI TWITTER
Ana ci gaba da ka-ce-na-ce kan batun gayyatar da Majalisar Wakilan Najeriya ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari don ya je ya yi mata bayani game da taɓarɓarewar tsaro a ƙasar kwanan baya.
Ranar 1 ga watan Disamba ne, majalisar ta yanke shawarar gayyatar Buhari don ya je zaurenta game da batun tsaro, sai dai a yanzu maganar ta sake tasowa bayan majalisar ta musanta cewa ta nemi afuwa kan gayyatar da ta yi wa Buhari.
Ta ce rahoton da wasu kafofin labarai suka fitar cewa 'ƴan majalisar sun roƙi afuwar shugaban ƙasar kan gayyatar da suka yi masa, ba gaskiya ba ne.
Sai dai, wani tsohon ɗan majalisa, Sanata Shehu Sani ya ce ai da ma tun farko ma tsoro ne ya sa majalisar ta janye sammacin da ta yi wa shugaba Buhari.
"Hakan ya nuna cewa da ma can gayyatar da suka yi masa, ba su yi ta da niyyar alheri ba," in ji shi.
Ya ce majalisa, kamata ya yi ta zama wani dandamali na wakiltar jama'a da tabbatar da ana gudanar da ayyukan gwamnati daidai tare da yin dokoki da sa ido kan ɓangaren zartarwa da na shari'ah.
Shehu Sani wanda sanata ne a Majalisar Najeriya ta takwas, ya ƙara da tambayar, mene ne amfani aika wa mutum gayyata, idan kuka san za ku janye daga baya?
Gayyatar dai na da alaƙa musamman da ƙaruwar hare-haren ƙungiyar Boko Haram, na baya-bayan nan da ya janyo gagarumin tashin hankali, shi ne kisan ƙare dangi na Zabarmari da ayyukan 'yan fashin daji.
Tsohon sanatan ya ce: "Shin wanne tsoro za ka ji a ƙasar da mutanen da kake wakilta, kullum a kashe su, a sace su, a kore su daga ƙauyukansu? Su sai da gonakinsu, su biya kuɗin fansa, tsoron me kake ji, (ba za) ka je ka yi magana da shugaban ƙasa (ba)?"
Ya goranta wa 'yan majalisar kan nuna tsoro da shakku cikin aikinsu na wakiltar jama'a.
'Dalilin da ya sa aka kau da gwamnatin Jonathan ke nan'
Shehu Sani ya ce "Ka gayyaci mutum, ya ce ba zai zo ba. Sannan ka janye, ka ce ka janye, kai ba ka ɗauki wani mataki na ƙin bin dokar da tsarin mulki ya ba ka iko ka yi ba?"
An tambayi tsohon ɗan majalisar ko ba ya ganin lamarin ya so ya zama siyasa har ma wasu na zargin cewa wani ɓangare na son yin amfani da damar don muzanta Shugaba Buhari.
"Ko siyaar ce, ai cikinta ake. Da siyasa, ake hawa kan mulki, kuma da siyasa ake mulki a Najeriya.
Yau, akwai suka da zarge-zarge da ake wa shugaban ƙasa na cewa wa'yannan abubuwa suna faruwa kamar bai damu ba. Ana kashe mutane, ana sace mutane, ana ci wa mutane mutunci," in ji shi.
A cewarsa, dalilin da ya sa aka kau da gwamnatin Jonathan ke nan, har wannan gwamnati ta hau.
Shin wannan ba dama ba ce a gare shi, ya faɗi abubuwan da yake yi da kuma abubuwan da yake so ya yi, Da kuma ƙalubale da yake fuskanta? Shehu Sani ya tambaya.










