Al-Shabab: Harin bam ya kashe mutun 10 a Somaliya

Manyan sojojin Somaliya na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su
Bayanan hoto, Manyan sojojin Somaliya na daga cikin wadanda harin ya rutsa da su
An wallafa

Hukumomi sun tabbatar da kashe mutun 10, tare da jikkata wasu da dama, a wani harin kunar bakin wake a filin wasan kwallon kafa da ke garin Galkayo.

An kai harin ne gabannin Firanminista Mohammed Hussein Roble, da shugaban yankin Ahmed Abdi Kariye su gabatar da bayanansu.

'Yansanda sun ce wasu manyan jami'an soji na cikin wadanda suka mutu a harin.

Sai dai kawao yanzu hukumomin ba su fitar da cikakken bayani kan wadanda harin ya rutsa da su ba.

Ƙungiyar Al Shabab da ke da mayaƙa a yankin ta dauki alhakin kai harin.

Harin na ranar Juma'a daya ne daga cikin jerin hare-haren da Al-Shabab ke kai wa a yankunan Somalia a baya-bayannan.

Ko a ranar takwas ga watan Agusta kungiyar ta kai irin wannan hari a sansanin sojin Somaliya da ke Mogadishu da ya kashe mutun 14.

Mafi yawan hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa sun fi mayar da hankali ne kan jami'an tsaro da kuma 'yan kasashen waje.