Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al-Shabab: Harin bam ya kashe mutun 10 a Somaliya
Hukumomi sun tabbatar da kashe mutun 10, tare da jikkata wasu da dama, a wani harin kunar bakin wake a filin wasan kwallon kafa da ke garin Galkayo.
An kai harin ne gabannin Firanminista Mohammed Hussein Roble, da shugaban yankin Ahmed Abdi Kariye su gabatar da bayanansu.
'Yansanda sun ce wasu manyan jami'an soji na cikin wadanda suka mutu a harin.
Sai dai kawao yanzu hukumomin ba su fitar da cikakken bayani kan wadanda harin ya rutsa da su ba.
Ƙungiyar Al Shabab da ke da mayaƙa a yankin ta dauki alhakin kai harin.
Harin na ranar Juma'a daya ne daga cikin jerin hare-haren da Al-Shabab ke kai wa a yankunan Somalia a baya-bayannan.
Ko a ranar takwas ga watan Agusta kungiyar ta kai irin wannan hari a sansanin sojin Somaliya da ke Mogadishu da ya kashe mutun 14.
Mafi yawan hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa sun fi mayar da hankali ne kan jami'an tsaro da kuma 'yan kasashen waje.