Manyan malaman addinai sun yi kira a haramta sauya ‘yan luwadi da madigo

.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Harry Farley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Manyan malamai fiye da 370 daga sassan duniya daban-daban suna kira a haramta sauya 'yan luwadi da madigo.

Malaman da suka yi wannan kira sun fito ne daga manyan addinan duniya da dama, kuma daga cikinsu fitattun masu goyon bayan auren jinsi daya ne.

Sun hada da Archbishop Desmond Tutu da kuma tsohon shugaban mabiya addinin Yahudu na Ireland David Rosen.

Sauran malaman addinin sun ce haramta sauya 'yan luwadi da madigo ka iya kallon fastoci a matsayin masu laifi.

Za a kaddamar da kiraye-kirayen haramta sauya masu auren jinsi guda ne a wajen taron da ofishin hulda da ƙasashen waje da hula da kasashen rainon Ingila da ci gaba zai gudanar ranar Laraba.

Bishop na darikar Anglican da ke Liverpool, Paul Bayes, da Mary McAleese, tsohuwar shugabar Ireland, na cikin wadanda suka sanya hannu kan takardar neman haramta sauya 'yan luwadi da madigo.

Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya jadda alkawarin da ya yi na haramta sauya 'yan luwadi da madigo inda a watan Yuli ya ce yin hakan "babban abin kyama ne" kuma "ba shi da mazauni a wannan kasar".

Ya zuwa yanzu gwamnati ba ta wallafa cikakken bayani kan haramta sauya 'yan luwadi da madigo ba sai dai ta ce ta kaddamar da bincike kuma za ta fitar da tsarin "idan lokaci ya yi".

Kasashe da dama sun haramta sauya 'yan luwadi da madigo, ciki har da Switzerland da wasu yankunan Australia da Canada da kuma Amurka.

2px presentational grey line

Sharhi - daga Ben Hunte - Wakilin BBC kan lamuran 'yan luwadi da madigo

Tun daga shekarar 2018, firaiministoci biyu na Birtaniya sun yi alkawarin haramta sauya 'yan luwadi da madigo amma har yanzu masu fafutuka na jira a dauki wannan mataki.

Daya daga cikin matsalolin haramta sauya 'yan luwadi da madigo ita ce yadda za a bayyana ma'anar "haramta sauya 'yan luwadi da madigo" da kuma yadda za ta shafi masu auren jinsi daya.

A yayin da alkaluman da gwamnati ta fitar suka nuna cewa an fi bai wa mata-maza shawarwari don sauya tunaninsu a tsakanin dukkan masu auren jinsi, wasu masu fafutuka na fargabar cewa kowanne sauyi daga bangaren gwamnati zai iya yin watsi da tsarin sauya masu jinsi na daban bisa la'akari da asalin jinsin mutum da kuma mayar da hankali kan kasancewarsa mace ko namiji.

Wasu kuma na fargabar cewa sauyin zai iya wuce gona da iri.

2px presentational grey line

'Na shiga cikin mawuyacin hali'

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 kan mutane 108,000 mambobin kungiyar masu auren jinsi daya ta Birtaniya ya nuna cewa an taba bai wa kashi biyu daga cikinsu shawara su sauya tunaninsu na jinsi.

Manyan addinai, ciki har da Kiristanci da Musulunci da Yahudanci, suna tunatar da mabiyansu cewa duk wata mu'amalar jima'i da aka yi ta ba tsakannin mace da namiji ba, ba ta halasta ba.

Joe Hyman, mai shekara 28, ya tashi a matsayin Bayahude a arewacin London. Ya ce an nemi yi masa rukiyya lokacin yana dan matashi.

Ya shaida wa BBC cewa "Ina so a yi mini rukiyya. Ba zan iya zama a matsayin dan luwadi ba kuma ni Bayahude ne. Ba na tsammanin iyayena za su yarda da hakan. Na shiga mawuyacin hali."

Ya ce ya tattauna da masu yin rukiyya ta shafukan intanet da kuma a zahiri da zummar sauya tunaninsa kan jinsinsa.

"Hakan ya sa na tsani kaina, na zama wanda ya sauya tunani game da jinsinsa, kuma a ko da yaushe ina cikin fargaba ina ganin abubuwan da nake yi ba daidai ba ne," in ji shi.

Joe Hyman

Asalin hoton, Joe Hyman

Bayanan hoto, Joe Hyman, wanda ka yi wa tiyatar sauya jinsi, ya ce hakan ya shafi lafiyar kwakwalwarsa

Malaman addinin sun yi kira a haramta duk wani nau'i na wa'azi da shawarwari kan sauya tunanin irin jinsin da mutum ke so ya zama.

Sai dai wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini daga bangaren addinai daban-daban sun ce haramta sauya 'yan luwadi da madigo zai yi karan-tsaye ga 'yancin mutane na addini.