Amurka: Trump ya ci gaba da yaƙin neman zaɓe

An wallafa

Shugaba Trump ya yi yaƙin neman zaɓe na farko a jihar Georgia tun bayan faɗuwa zaɓe, a wani mataki na mara baya ga ƴan takarar maajalisar dattawan ƙasar daga jihar Georgia da za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓensu a watan Janairu.

Shugaban ya faɗa wa dandazon mutanen da suka taru a Valdosta cewa shi ne ya lashe zaɓen jihar da aka gudanar, duk da cewa ba shi aka sanar a hukumace ba.

Duk da ya yi zargin an tafka maguɗi a zaɓen, ya bukaci magoya bayansa su fita su jefa ƙuri'unsu, sannan kar cuwacuwar da yake cewa an yi ta rage musu ƙwarin gwiwar samun nasara a zaben.

Ya ce Amurka za ta faɗa hannun ƴan gurguzu matsawar jam'iyyar Democrat ta lashe kujeru biyu na ƴan majalisar da za a kara a kansu.

Wasu magoya bayan jam'iyyar Republican na fargabar cewa ci gaba da zargin tafka maguɗi a zaɓen da Mista Trump ke ta faman yi har zuwa yanzu na iya sa wa su kasa samun nasara a zaben da yake da matuƙar muhimmanci.

Fargabar ita ce, masu zaɓe na iya fitar da rai da cewa za a yi adalci a zaɓen, sakamakon kalaman da shugaban na Amurka ke ci gaba da furtawa.

Tun farko, shugaban ya yi ƙoƙrin ganin gwamnonin jihohin da yake zargin an yi maguɗi a cikinsu waɗanda na Republican ne sun taimaka masa domin yin watsi da sakamakon zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Republcan ce ke jagoranci a wasu jihohi a zaben majalisar dokoki, ana gudanar da bincike na musamman kan zargin maguɗi a zaben da kwamitin yaƙin neman zaben shugaba Trump ke yi.

Kotuna da dama a sassan kasar daban-daban sun yi watsi da iƙirarin cewa an samu kura-kurai, ko ma wata ƙulla-ƙulla da sunan taimaka wa jam'iyyar Democrat ta su Zababben Shugaba Joe Biden.