Zaɓen Amurka: Shugaba Trump ya amince ya bar Fadar White House

An wallafa

Shugaba Trump ya ce zai bar Fadar White House idan aka tabbatar da Joe Biden a hukumance a matsayin shugaban kasa, yayin da wakilan masu zabe za su tabbatar da ƙuri'unsu a watan gobe.

Trump ya yi wannan kalami ne - yayin amsa wannan tambayar da wani dan jarida ya yi masa: "Idan masu zabe suka tabbatar wa zababben Shugaba Joe Biden nasara, shin ba za ka fice daga fadar nan ba kenan?"

Sai shugaban ya ce: "Domin ku sani...tabbas zan fice, tabbas zan fice kuma kun san haka. Amma ina ganin akwai wasu abubuwa masu yawa da ke faruwa daga yanzu zuwa 20 ga watan Janairu."

Wadannan kalamai ne mafi kamanceceniya da amincewa da shan kaye da shugaban ya yi tun bayan faduwarsa zabe.

Ya riƙa zargin cewa an tafka magudi a zaɓen ba tare da ya bayar da wata cikakkiyar hujja da za ta tabbatar da iƙirarin nasa ba.

Mista Trump ya ci gaba da cewa zai zama "abu ne mai matukar wahala" ya amince cewa ya sha ƙasa, kana ya ƙi amsa tambayar ko zai sake tsayawa takara a zaben ƙasar mai zuwa.

Ya kuma ce zai gudanar da wani gangami a jihar Georgia a ranar Asabar, don mara wa 'yan jam'iyyar Republicans biyu baya don samun nasarar zama sanatoci.

A baya dai shugaban ƙasar ya ƙi amincewa gwamnatinsa ta fara shirin miƙa mulki ga Joe Biden wanda ya yi nasara, ko da yake ya sauya shawara daga bisani.

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Joe Biden, ya ce kwamitin karɓar mulkinsa na samun cikakken hadin kai daga gwamnatin Shugaba Trump, bayan amincewa da nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da ya gabata.

Yayin wata hira da kafar talabijin din NBC, Mista Biden, ya ce suna samun sahihan bayanai dangane da sha'anin tsaron kasar da kuma abin da ya shafi annobar korona.

Sai dai ya ce har yanzu bai yi wata magana da Shugaba Trump ba, wanda ke ci gaba da musa cewa ya sha ƙasa a zaɓe.