Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan Afirkan da ke da tarihin cin ƙwallo fiye da Ronaldo da Messi a Kofin Duniya
Cristiano Ronaldo ya kasance wanda ya zura ƙwallo a Gasar cin Kofin Duniya daban-daban har shida da ya halarta, tarihin da ya zuwa yanzu babu wanda ya kafa shi.
Haka shi ma Lionel Messi, mai shekara 39 ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a Gasar Kofin Duniyar, inda zuwa yanzu ya ci 18.
Lokacin da Ronaldo ya fara cin Uzbekistan a wasa na biyu a cikin rukuni da Portugal ta zazzaga 5-0, ya zama na biyu mafi tsufa da ya taɓa zura kwallo a raga a tarihin Gasar Kofin Duniya, yana da shekara 41 da kwana 138.
Sai dai duk da wannan ƙoƙari da suka yi ba su kamo tarihin ɗan wasan Kamaru ba a Gasar Kofin Duniya.
Ronaldo da Messi ba su kai ƙwazon da tsohon ɗan wasan tawagar Kamaru, Roger Milla a wannan fannin.
Wane tarihi Roger Milla ya kafa?
Milla ya fara taka rawar gani a Gasar Kofin Duniya a 1982 da aka buga a Sifaniya.
Sunansa ya shahara a duniya yana da shekara 38, sakamakon ƙwallo huɗu da ya zura a raga, lokacin da tawagar Indomitable Lions ta kai zagayen kwata-fainal a wasannin da Italiya ta shirya a 1990.
Hakan ya sa Kamaru ta zama ƙasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta kai wannan matakin - Inda Milla ke murnar cin ƙwallo da yin rawa yana jijjaga ƙugu ya kuma kama tutar da take kafe a kusurwa fili - hakan ya sa yana nishandar da ƴan kallo, kuma shi kaɗai ke wannan salon.
Shekara huɗu bayan nan, Milla ya sake zura ƙwallo a Gasar cin Kofin Duniya a Amurka da 1994, ya kuma yi wannan ƙwazon tun daga nesa, inda ya ci Rasha.
Rawar nan da yake yi ya kama tutur kusurwar fili yana rawa da jijjiga ƙugu ita dai ya ci gaba da yi, amma Kamaru ta sha kashi da ci 6-1, sannan ta fice daga gasar a matakin cikin rukuni.
Duk da haka, babu shakka Ronaldo zai yi alfarin cewa ya ture Messi daga matsayi na uku zuwa da na huɗu a jerin dattawan da suka ci ƙwallaye a tarihin Gasar Kofin Duniya, bayan da ƙyaftin ɗin Argentina ya ci ƙwallo yana da shekaru 38 da kwana 363 a nasarar da Argentina ta doke Austria a wasa na biyu a cikin rukuni.
Haka kuma Messi zai iya ƙara yin ƙasa a jadawalin da zarar ɗan wasan Bosnia-Herzegovina, Edin Dzeko ko ɗan ƙasar Croatia, Luka Modric, dukansu masu shekara 40, suka zura ƙwallo a wannan gasar da ake yi a Amurka da Kanada da kuma Mexico.
Ɗan wasan tawagar Japan, Yuto Nagamoto ma ya girmi Messi na Argentina da wata tara da haihuwa, sai dai har yanzu ba a saka shi a wasa ba.
Watakila a fannin masu tsaron raga a samu wani gwarzon da ba a zata ba, wanda zai iya cin ƙwallo a gasar, waɗanda sun girmi Messi a shekarun haihuwa, daga ciki har da Manuel Neuer na Jamus da Vozinha na Cape Verde da Fernando Muslera na Uruguay - To sai dai kuma ba a taɓa samun mai tsaron raga ya ci ƙwallo ba a raga daga gasa 22 da aka buga a tarhihin Kofin Duniya.
Ɗan wasan Austria, Marko Arnautovic, mai shekara 37, ya shiga cikin goman farko daga cikin masu yawan shekarun haihuwa da ya ci ƙwallo a gasar, ya kuma yi haka ne a bugun fenaritin da ya ci Japan.
Da alama, wannan tarihin da Roger Miller ya kafa zai ci gaba da tabbata a matakin dattajin da ya fara cin ƙwallo a gasar Kofin Duniya, har sai idan Ronaldo da Messi za su buga gasar da za a yi a 2030, sannan su ci ƙwallo a haɗakar da za a yi tsakanin Sifaniya da Portugal da Morocco da kuma Uruguay da Argentina da Paraguay
Ko hakan zai iya yiwuwa kuwa?
Jerin dattawa 10 da suka ci ƙwallo a tarihin Gasar Kofin Duniya
1. Roger Milla - Kamaru da Rasha (28 ga Yunin 1994) - Shekara 42 da kwana 39
2. Cristiano Ronaldo - Portugal da Uzbekistan (23 ga Yunin 2026) - Shekara 41 da kwana 138
3. Pepe - Portugal da Switzerland (6 ga Disamban 2022) - Shekara 39 da kwana 283.
4. Lionel Messi - Argentina da Austria (22 Yunin 2026) - Shekara 38 da kwana 363.
5. Gunnar Gren - Sweden da Germany (24 ga Yunin 1958) - Shekara 37 da kwana 236.
6. Cuauhtemoc Blanco - Mexico da Faransa (17 ga Yunin 2010) - Shekara 37 da kwana 151.
7. Felipe Baloy - Panama da England (24 ga Yunin 2018) - Shekara 37 da kwana 120 .
8. Marko Arnautovic - Austria da Jordan (17 ga Yunin 2026) - Shekara 37 da kwana 58.
9. Obdulio Varela - Uruguay da England (26 ga Yunin 1954) - Shekara 36 da kwana 279.
10. Martin Palermo - Argentina da Girka (22 ga Yunin 2010) - Shekara 36 da kwana 227.