MDD: Yakin Tigray na kawo jinkiri ga ayyukan jin kai a arewacin Habasha

An wallafa

Fada da ake ci gab da gwabzawa a yankunan Tigray na yi wa shirin raba kayan agaji kafar ungulu inji Majalisar Dinkin Duniya.

Miliyoyin jama'a na fuskantar rashin abinci da magani.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun sanar wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa har zuwa Juma'a babu hanyar shiga yankin tabbatacciya domin raba wa mutanen kayan agaji.

Dakarun gwamanatin tarayyar Habasha sun kutsa cikin yankin na Tigray ne a karshen makon jiya, har sun shiga Mekelle babban birnin yankin.

BBC ta sami damar yin magana da wani mutum a Mekellen kuma ya tabbatar cewa "har yanzu ana fada a yankunan da ke kusa da birnin". Gwamnatin yankin ta TPLF ma ta ce ana can ana gwabzawa.

Ministan Habasha mai kula da yada dimokradiyya Zadig Abraha ya yi watsi da bayanan, yana cewa babu wani yaki cikin yankin.

Dakarun TPLF sun janye daga Mekelle domin rage tasirin hare-hare daga sojin gwamnati kan jama'ar birnin, amma ana can ana yfada a yankunan da ke wajen birnin.

Sai dai jkungiyar ta TPLF ta ce a shirye ta ke ta tattauna.

"Duk da ba za mu mika wuya kan batun ba, amma muna kan bakar mu ta samar da zaman lafiya," inji TPLF.