Rikicin Tigray: Dakarun Habasha sun ce sun ƙwace ikon yankin Tigray

An wallafa

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya ce dakarun gwamnati sun karbi ikon babban birnin yankin Tigray.

Tun da farko dakarun gwamnatin sun shiga Mekelle inda suka buɗe wuta a kan dakarun da ake fafatawa da su na yankin Tigray.

Jagoran jam'iyyar TPLF ta yankin Tigray ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa, za su ci gaba da fafutukar da suke wajen ganin sun kare 'yancinsu tare da tabbatar da shi har sai abin da hali ya yi.

An dai kashe daruruwan mutane inda wasu da dama kuma suka tsere suka bar muhallansu a rikici tsakanin dakarun gwamnatin Habasha da na jam'iyya mai mulkin yankin Tigray ta TPLF.

An fara rikicin ne tun a farkon watan Nuwambar 2020, bayan da Mr Abiy ya sanar da cewa dakarun gwamnati za su kai hari kan dakarun Tigray bayan ya ambata cewa an kai wa sansanonin soji hari.

An samu rikici sosai da hare-haren sama tun daga lokacin.

Me Gwamnati ta ce game da yankin Tigray?

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Mr Abiy ya ce dakarun gwamnati sun karɓe ikon yankin.

Ya ce: "Ina mai farin cikin sanar da ku cewa mun kammala aikinmu saboda mun ƙwace ikon yankin Tigray, yanzu dakarunmu sun cimma nasarar abin da muke so".

Dakarun gwamnatin sun saki dubban sojojin da dakarun TPLF suka sace, sannan kuma sun samu karɓe ikon tashar jirgin saman yankin da ma wasu manyan ofisoshi a yankin.

Mr Ahmed, ya ce duk da dakarun nasu sun yi taka tsan-tsan da fararen hular da ke yankin, amma akwai fargabar da suke da ita na mutane dubu 500 ɗin da ke cikin babban birnin yankin da aka ƙwace ikonsa.

Firaministan ya ce, yanzu babban aikin da ke gabansu shi ne yadda za a sake fasalta birnin da ma yankin da aka lalata da kuma yadda za a dawo da mutanen da suka tsere daga muhallansu saboda rikicin gida.

To sai dai kuma a ciki wani sako da jagoran jam'iyyar TPLF ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Reuters, bai yi wani cikakken bayani a game da halin da ake ciki ba, sai dai ya ce irin abubuwan da dakarun gwamnati ke yi to zai kara rura wutar rikicin ne kawai.

Me Majalisar Ɗinkin Duniya ke cewa kan rikicin?

Tuni dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa za a iya samun aikata laifukan yaƙi matukar dakarun gwamnatin Habasha suka kai hari Mekelle.

Kazalika ta bayyana damuwa a kan rashin hanyoyin isar jami'an agaji wurin da rikicin ya tsananta.

To sai dai kuma mahukuntan ƙasar ta Habasha sun ce za a buɗe hanyoyin shigar da kayan agaji sannan kuma gwamnatin za ta yi aiki tare da hukumomin agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya domin kare rayuka da dukiyoyin fararen hula.

Fiye da mutum 40,000 sun tsere daga Habasha tun da rikicin ya fara.

Ranar Alhamis dakarun Habasha sun tsare kan iyakar yankin da Sudan inda suka hana masu tserewa daga rikicin shiga ƙasar domin samun mafaka, kamar yadda wasu 'yan gudun hijira ke cewa.