Masarautar Zazzau: Me ya sa El-Rufa'i ya dakatar da Waziri Ibrahim Aminu

Asalin hoton, Zazzau Emirate
Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da matakin da gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ɗauka na dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu daga kan muƙaminsa.
Shi dai Wazirin Zazzau ya kasance ɗaya daga cikin mutum biyar da ke zaɓen Sarki a masarautar, kuma an dakatar da shi ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da ƙalubantar nadin Ambasada Ahmadu Bamalli a gaban kotu, a matsayin sabon Sarkin Zazzau na 19.
Tun a makon jiya ne ake ta yayata sanarwar dakatar da Wazirin Zazzau ɗin Alhaji Ibrahim Aminu a shafukan sada zumunta, inda aka ambato babban sakatare a ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar Kaduna, Musa Adamu a matsayin wanda ya sanya hannu a takardar dakatarwar a madadin kwamishina mai kula da ma'aikatar Jafaru Sani.
Wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin jama'a a tare da zazzafar muhawara kan dalilan da suka sa aka dakatar da basaraken.
Yayin da wasu ke danganta matakin a kan rashin halartar Wazirin wani taro da ma'aikatar kula ƙananan hukumomi da masarautu ta gayyace shi, wasu kuwa cewa suke an dakatar da shi ne saboda ya ƙi amincewa ya sauya matsaya kan wanda gwamnan jihar ke son ya zama Sarki.
Abin da ya faru a lokacin da masu zaɓen Sarki wanda Wazirin na Zazzau ya jagoranta suka miƙa sunayen mutum uku waɗanda kuma cikin su, babu wanda gwamnan jihar ke so.
Wani ƙaulin kuma na cewa, ƙin amincewar Wazirin na Zazzau na sauya lauyan da ke kare shi a sharia'ar da ake yi kan naɗin Sabon Sarkin wanda shi kansa Wazirin tare da sauran masu zaɓen Sarki ke cikin waɗanda ake ƙararsu.
A ɓangare guda kuma wasu rahotanni na cewa, an dakatar da Wazirin na Zazzau ne saboda zargin sa a kan kwarmata wa 'yan jaridu takardar da masu zaben Sarkin suka gabatar wa gwamnatin jihar na wadanda suka zaba domin ya gaji Marigayi Dr Shehu Idris.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Wazirin Zazzau ɗin Alhaji Ibrahim Aminu kan wannan batu amma ba a samu ba, yayin da kuma dukkan jami'an da muka tuntuɓa a ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu, suka ƙi amincewa su yi magana da Yusuf Tijjani na BBC Hausa.

"Zubewar ƙimar masarauta"
Wasu masu sharhi irin su Dr Nasir Aminu, na Jami'ar Cardiff a Birtaniya na ganin dakatar da Wazirin na iya shafar ƙimar masarautar.
Ya ce: "Sarautar Waziri sarauta ce babba a Zazzau. To amma ta kai a yau gwamnati tana dakatar da wannan sarauta, lallai abin da ban tsoro kuma hakan ya rage ƙimar Masarautar Zazzau.
"Idan aka fara kwaikwayon wannan a sauran masarautu na arewa, to wata rana za mu tashi mu ga ba masarautun nan, saboda za a kori kowa ƴan siyasa kuma za su kawo mana waɗanda za su gaya musu abin da suke so su ji, ba wai waɗanda za su yi aikin gaskiya ba," in ji shi.
To sai dai wasu muƙarraban gwamnan jihar Kaduna sun kare matakin dakatar da Wazirin na Zazzau -- suna cewa hakan bai saɓa ƙa'ida ba.
Muhammad Lawal Shehu da ake yi wa laƙabi da MOLASH, na daga cikin mataimaka na musamman ga gwamnan jihar Kaduna kan harkokin da suka shafi siyasa.
A cewarsa "Ita maganar tsarin aikin gwamnati idan ta zo ana duba wane laifi ka yi ne kuma wane irin hukunci ya dace a yi maka. Ina ga abin da ya faru kenan a maganar Wazirin Zazzau. Ba wani abu ne na maganar siyasa ko wani abu daban ba."
Shi dai gwamna jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai a lokacin da yake jawabi wajen bikin miƙa sandar girma ga Sarkin ya ce gwamnatin ta kudiri aniyar yi wa tsarin Masarautu na jihar garanbawul inda ake duba yuwuwar ɓullo da tsarin karba-karba a masarautun da ke da gidajen Sarauta fiye da daya.
Ƙarin labarai masu alaƙa
Gwamnan ya ce ya naɗa Ambasada Ahmad Bamalli ne domin gyara rashin adalci da Turawan Mulkin Mallaka suka yi wa daya daga cikin gidajen Sarautar Zazzau.
Sai dai Dr Nasir Aminu na cikin masu ra'ayin cewa akwai lauje cikin naɗi. "Idan har zai gyara abubuwan da suka faru a shekara 100 da suka gabata, to me zai sa ba zai gyara abubuwan da suka faru a shekara 163 da suka wuce ko na fiye da shekara 200 ba," in ji shi.
Ya ƙara da cewa: "Masarauta gidan al'adunmu ne, daga nan ake tarbiyya, kuma duk inda ta ƙwace a haka ba mu san halin da za a shiga ba."
To sai dai Molash ya sake cewa kamata ya yi a kyautawa gwamnatin jihar zato. "Shi dama tsarin sarauta akwai wanda idan an bayar za ka ga wasu bai musu daɗi ba, akwai kuma wanda shi a lokacin yake murna.
"Kuma kamar yadda gwamna ya faɗa ya yi wannan abin ne bisa ga tunanin adalci, kuma Allah ya ga zuciyarsa. Idan ya yi adalci Allah na kallon zuciyarsa idan ma bai yi ba Allah na gani, amma abin da nake so da mutame su kyautata masa zato."
Gwamnatin jihar dai ta dakatar da basaraken ne wanda shi ne na biyu mafi girmar mukami a masarautar, a dai dai lokacin da ake ci gaba da shari'a a gaban kotu kan zaben Sarkin, lamarin da ke ci gaba da janyo martani daga ɓangarori da dama.












