Sarkin Zazzau: Abu 4 da suka faru tun bayan rasuwar Sarki Shehu Idris

SARKIN ZAZZAU

Asalin hoton, INSTAGRAM/MAJEEDA-STUDIO

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya musamman daga masarautar Zazzau na jiran sanarwar wanda zai gaji marigayi Sarki Alhaji Shehu Idris wanda ya rasu yana da shekara 84 a duniya.

Tun rasuwar sarkin a ranar Lahadi ake ta canki-canka kan wanda ake gani zai iya zama sabon sarki, inda wasu ke cewa tsarin naɗa sabon sarkin na tafiyar hawainiya.

Bisa tsarin sarautar Zazzau ana zaɓen sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda huɗu. Akwai Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sulluɓawa.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ne zai zaɓi sabon Sarkin Zazzau, cikin mutum uku daga cikin ƴaƴan gidan masarautar Zazzau da masu naɗin sabon sarki za su tura masa.

Wannan layi ne

Abubuwa da dama sun faru tun bayan mutuwar sarkin. Ga wasu daga cikinsu:

Masu zaɓen sarki sun killace kansu

A bisa al'ada masu zaben sarki na killace kansu na tsawon wani lokaci suna nazari da tantancewa kafin majalisarsu ta zaɓi sarki - ana karantawa ƴan majalisar ƙa'idojin zaɓar wanda zai zama sarki da suka haɗa da:

  • Ya kasance bai taɓa yin laifi wanda hukuma ta kama shi ko ta hukunta shi ba.
  • Ya taɓa rike matsayi na sarauta ko hakimta a Zazzau
  • Samun cikakken ilimin zamani da na addini
  • Ya kasance ba mai yawan shekaru ba wato kada ya kasance tsoho tukuf
  • Tabbatar da cewa ya fito daga gidajen sarauta guda huɗu.

Sannan sai a tantance sunaye a majalisar zaɓar sarki, a aike wa gwamna sunayen kafin sanar da sabon sarki

'Ina karanta littafin wani Bature kan zaben sabon Sarkin Zazzau'

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce yayin da ya ke jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani tsohon littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.

A shafinsa na Twitter, El-Rufa'i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken "Gwamnati a Zazzau" wanda aka buga a 1960.

Gwamna El- Rufa'i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

'Ba na iya bacci sai na sha magani tun bayan rasuwar sarkin Zazzau'

Gwamnan ya kuma bayyana cewa tun ranar Lahadi da aka sanar masa da rasuwar Sarkin Zazzau, bai sake bacci ba sai ya sha magani saboda baƙin ciki.Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron addu'ar uku na Marigayi Mai martaba Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi.Manyan mutane da da suka halarci addu'ar uku da aka yi sun hada da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru, da Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da na Filato Simon Lalong.

Wannan layi ne

Yadda Addu'ar uku ta kasance

Daga cikin manyan mutane da aka gani a wurin addu'ar sadakar ukun marigayi Alhaji Shehu Idris akwai tsoffin shugabannin Najeriya, da shugabannin majalisar dokokin tarayya, da sarakuna da manyan jami'an gwamnati.

Kaduna

Asalin hoton, TWITTER/@GOVKADUNA

Kaduna

Asalin hoton, TWITTER/@BELLOMATAWALLE1

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa'ad da Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero suma sun jajanta wa Masarautar Zazzau, akwai kuma mai Martaba Sarkin Rano Kabiru Muhammad Inuwa, da Mai Martaba Sarkin Gombe Dr. Abubakar Shehu Abubakar tare da Mai Martaba Sarkin Hadejia Alh. Dr. Adamu Abubakar Maje a wajen ta'aziyyar Sarkin Zazzau

KADUNA

Asalin hoton, SAUDAT PHOTOGRAPHY

Wasu labaran da za ku so karantawa

Wannan layi ne