Biden: 'Mutane na iya mutuwa' yayin da Trump ke jan ƙafa wajen miƙa mulƙi

Asalin hoton, Joe Raedle
Joe biden ya gargadi Amurkawa cewa "mutane na iya mutuwa" idan Shugaba Trump ya ci gaba da hana shi bayannan da yake bukata na shirin karbar mulki.
Yayin wani jawabi da yayi a Delaware, zababben shugaban kasar ya ce ana bukatar hadin kai domin magance matsalar sake barkewar cutar korona.
Ya kira halayyar Shugaba Trump ta kin amincewa ya sha kaye a zaben, duk kuwa da cewa bangarorin siyasar kasar biyu sun bukaci da yayi haka, inda ya kira matakin "cike da rashin sanin ya kamata."
"Wannan ba wasan yara ne ba," inji uwargidan tsohon shugaban Amurka Obama, a wani sakon da ta wallafa a shafukan sada zumunta.
Zababben shugaba Biden na da kuri'u 306 na wakilai masu zaben, wanda ya zarce 207n da ake bukata dan takara ya samu kafin ya lashe zaben shugaban kasa.
Amma duk da haka Mista Trump, wanda dan jam'iyyar Republican ne, ya ki amincewa da sakamakon zaben, kuma ranar Litinin ya wallafa wani sakon Tiwita yana cewa,: "Ni na lashe zaben".







