Zaben Amurka na 2020: Biden ya yi nasara. Me zai faru a yanzu?

Asalin hoton, Getty Images
Joe Biden ya samu kuri'u 270 da yake bukata na wakilan kwamitin zaɓe da ake kira electoral college wajen ɗare karagar mulki, bayan fintinkau da ya yi wa shugaba Donald Trump a takarar shugabancin ƙasar. Yanzu me zai faru?
Yanzu dai ba lokaci ba ne da tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai kwashe kayansa ya nufi gida mai lamba 1600 a kan titin Pennsyvania ba - akwai wasu abubuwan da ake bukatar soma aiwatarwa da farko.
Bisa al'ada yanayi ne mai sauki, sai dai a wannan lokaci ya zo da wasu 'ƴan matsaloli saboda kararrakin da aka shigar da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen.

Yaushe Joe Biden zai karɓi mulkin ƙasa?
Kamar yadda yake a rubuce a kundin tsarin mulkin Amurka, sabon wa'adin shugaban ƙasa na soma wa ne daga 20 ga watan Janairu da rana.
Ana mika mulki ne a bikin rantsuwa da ake gudanarwa a birnin ƙasar, Washington DC. Sabon shugaban ƙasa da mataimakinsa na shan rantsuwar kama aiki ƙarkashin babban alƙalin kotun ƙoli.
Don haka ana sa ran ganin Joe Biden da Kamala Harris sun kama aiki a ranar 20 ga watan Janairun 2021.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan na iya sauyawa. Idan shugaban ƙasa ya mutu a kan mulki ko murabus, za a rantsar da mataimaki a cikin gaggawa.

Me ake nufi da ƙarbar mulki?
Wannan lokaci ne tsakanin bayanan sakamakon zaɓe da soma shirye-shiryen karɓar mulki a ranar 20 ga watan Janairu.
Shugaba mai jiran gado na kafa kwamiti ko tawagar da ke shirin karbar mulki da zarar an rantsar da shi - kuma tuni tawagar Biden ta kafa shafin intanet na karbar mulki.
Su zasu zaɓi 'ƴan majalisar ministoci, tattauna tsare-tsaren da za a bai wa muhimmanci da kuma shirin soma mulki.

Asalin hoton, Reuters
Mambobin kwamitin na ziyartar ma'aikatun gwamnati domin samun bayanai da kuma sanin halin da ake ciki, kasafin su da tsarin ayyukan ma'aikata.
Ƙwamitin na tattara bayanan sabbin ma'aikatan da za su shigo da kuma taimakawa har bayan rantsuwar kama aiki. Wasu daga cikinsu na iya ci gaba a dama da su a mulkin.
A 2016, Shugaba Barack Obama ya gana da wanda ya gajeshi Donald Trump a Ofishin shugaban kasa da ake kira Oval Office, hotunan sun nuna yadda babu wata musabaha a tsakaninsu.
Joe Biden ya shafe watanni ya na zabo mutanen da zasu masa aiki a kwamitin karban mulki, ya nemi tallafin kuɗaɗe rike kwamitin kuma a makon da ya gabata ya ƙaddamar da shafin intanet kan hakan.

Wadanne kalmomi za ake yawaita ji a yanzu?
Zababben shugaban ƙasa: Idan ɗan takara ya yi nasarar zaɓe kuma yana jiran rantsuwar kama aiki a ranar 20 ga watan Janairu, sunan da za a ke kiransa da shi kenan.
Majalisa: Joe Biden nan bada jimawa ba za a ji yana sanar da mutanen da yake so a majalisar ministocinsa, wanda shi ne jigo ga kowacce gwamnati. Sun hada da mutanen da za su jagoranci manyan ma'aikatu da hukumomi.
Zaman tantacewa: Da dama daga cikin manyan naɗe-naɗen gwamnati da shugaban zai yi dole ya nemi amincewar majlisar dattijai. Mutanen da Mr Biden zai zaɓa dole su bayyana gaban majalisa domin amsa tambayoyi kwamitoci majlisar dattijai, inda za a jefa kuri'a amincewa ko watsi.
Celtic: A matsayinsa na zababben shugaban kasa, Mr Biden zai samu karin tsaro sosai kuma sunansa na sirri zai koma Celtic. .Ƴan takara ke zaɓen wannan suna. Mr Trump a lokacin ya zaɓi Mogul, ita kuma Kamala Harris ta zaɓi Pioneer.

Ko akwai wasu ƙalubalen shari'a?
Kusan za a iya cewa dole a samu. Shugaba Trump dai ya sha alwashin cewa sai ya ƙalubalanci dukkan sakamakon zaɓen jihohin nan hudu da aka fafata a kansu wadanda kuma Biden ya samu nasara a kansu.
Trump ya yi zargin cewa an tabka maguɗi a wadannan jihohin.
Wasu rahotanni sun ce a yanzu haka kwamitin yaƙin neman zaben Trump ya fara neman ƙwararrun lauyoyi da za su jagoranci shari'ar ta su.

Me zai faru idan Trump yaƙi amincewa da shan kayi?
Dagamai aiko mana da rahoto daga North America Anthony Zurcher
Donald Trump dai ya sha nanata cewa zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen Idan har wannan yunkuri nasa ya ci tura ma'ana bai samu nasara ba, to ko shakka babu zai fuskanci matsin lamba a kan sai ya amsa cewa ya sha kayi. Abin tambayar shi ne zai yi hakan?
Kiran waya daga wanda ya sha kayi a zaɓe ya kira wanda ya samu nasara don yi masa murna wata al'ada ce da ake girmamawa a tsarin siyasar Amurka, za a iya cewa ta zama ma wajibi.
A Misali a shekarar 2018, ƴar takarar gwamna a jam'iyyar Democrats Stacey Abrams ta ce an mata maguɗi kuma bata amshi kayin da ta sha ba daga Brian Kemp.
Irin haka bai taɓa faruwa a tsarin siyasa ta ɓangaren zaɓen shugaban ƙasa ba.
Duk da cewa Mr Trump bai amshi kayin da ya sha ba, sannan bai nuna alamar halartar rantsar da Biden ba, dole ne ya na da wasu ka'idoji da ya kamata ya bisu wanda su ne dole ya shirya mika dukkan wasu al'amuran da suka shafi mulkin ƙasar ga wanda ya samu nasara shi da muƙarrabansa, abin da a cewar wasu jami'an Trump suka ce tuni sun yi wannan.

Me Kamala Harris za ta yi, yayin dakon karɓar mulki?
Kamala Harris, ita ce mace ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa, don haka zata naɗa nata ma'aikatan tare da koyon sanin makamar aikinta ta la'akari da gwamnatocin da suka shuɗe.
A ka'ida dai mataimakin shugaba ƙasa na aiki ne a fadar gwamnatin ƙasar, amma kuma baya zama a nan. A bisa al'ada mataimakin shugaban ƙasar Amurka na zama ne a wani waje da ke da tazarar tafiyar minti 10 daga fadar shugaban ƙasar.
Mijinta Doug Emhoff, dai lauya ne da yake aiki a wata masana'anta.

Asalin hoton, Getty Images
Tana da 'ya'ya biyu a aurenta na farko data yi sune Cole da Ella.

Ya shigar Fadar White House ta ke kasancewa?
Yanayin a yanzu da ɗan dama-dama ba kamar a shekarun 1800 lokacin da shugaban ƙasa na farko mai aure John da Abigail Adams suka shiga fadar - ginin bai kammala ba.
A wannan zamanin ana saran sabon shugaban ƙasa da iyalansa su sauya fasalin adon gidan da kayayyakin da ke ciki ko wadanda suka tsufa ko yage, don haka majalisa na ware kuɗin wannan hidima.
Akwai dakuna 132 da bundaƙi 35 da ke bukatar a kula da su a cikin fadar.
Uwar gida Melania Trump, da ke da ƙwarewa a fannin ado da kayan ƙawa, ta jagoranci sauya fasalin gidan kuma ita ke kula da duk wani gyara da bikin ƙaddamar da adon kirismeti.











