Yadda ƴan gudun hijrar Mali suka rungumi sana'oin dogaro da kai a Nijar

'Yan gudun Hijra
An wallafa

Wasu 'yan gudun Hijrar Mali a Jamhuriyar Nijar sun rungumi sana'oin dogaro da kai don taimaka wa kansu da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa. .

Matan waɗanda wata ƙungiya ta horar kan yadda ake sarrafa kayayakin kare kai daga ɗaukar cutar korona kamar takunkumi da sabulun kashe ƙwayoyin cuta, na wanka da wanki sun ce sana'o'in sun buɗe musu hanyoyin inganta rayuwarsu da kuma ta 'ya'yansu.

Hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta dauki nauyin koyar da matan wannan sana'a a kokarin hukumar na samar musu da ayyukan dogaro da kai.

Matan sun samu horon ne ta hanyar kungiyar Furjia, sannan daga bisani suka rarraba kansu zuwa wasu kungiyoyi na mata da hukumar kula da 'yan gudun hijrar ke daukar nauyi.

Wata jami'a a kungiyar ta shaida wa BBC cewa, na horar da matan sana'oin ne domin su dogara da kansu, sannan kuma da la'akari da cewa ba kowa ne zai iya siyan abubuwan kare kai daga cutar korona ba.

Daya daga cikin matan da suka samu horon kuma 'yar gudun hijra ce daga Mali ta shaida wa BBC cewa da wannan sana'a da ta koya a yanzu wasu daga cikin matsalolinta musamman na kula 'ya'yanta biyar sun gushe.

Ta ce,"Da wannan sana'a dana koya nake kuma yi, ina yin komai da kai na 'ya'yana yanzu basu da matsala domin ina musu komai da suke bukata don muna ci muna sha har ma da sauran bukatu".

Itama daya matar da ta samu wannan tagomashi, ta shaida wa BBC cewa, ita da yaranta biyu da suka zo daga Mali yanzu sai hamdala, saboda tana yiwa yaran nata komai kuma har makaranta a yanzu ta saka su suna zuwa.

Hukumar dake kula da 'yan gudun hijrar ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce, baya ga wadanna 'yan gudun hijra data bawa horo a Yamai, zata ci gaba da bawa sauran 'yan gudun hijrar da ke zaune a wasu sassa na Nijar irin wannan horo ta yadda zasu rinka dogaro da kansu.