Mata 11 sun mutu a turmutsutsun neman biza a Afghanistan

A crowd of men holding up their passports

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban mutane ne suka taru don karɓar biza
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A ƙalla mata 11 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a yayin wata turmutsutsu da aka yi a wani filin wasa Afghanistan, inda mutane ke neman biza, a cewar hukumomi.

Lamarin ya faru ne bayan da ''dubban mutane'' suka taru don neman izinin shiga Pakistan, a cewar wani mai magana da yawun hukumomin yankin.

An ce wa mutanen su je filin wasan ne maimakon ainihin inda ake neman bizar da ke birnin Jalalabad.

An buɗe bayar da bizar Pakistan ne bayan shafe wata bakwai da aka yi na dakatar da hakan sakamakon annobar cutar korona.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce: ''Masu neman bizar sun yi ta ƙoƙarin samun shaida ne daga jami'an ofishin diflomasiyya,'' a cewar wani jami'i a Jalalabad.

''Daga nan sai lamarin ya rincaɓe har aka fara turereniya.''

Jakadan Pakistan a Afghanistan, Mansoor Ahmad Khan, ya ce ''ya ji matuƙar ɓacin rai'' kan lamarin kuma ƙasarsa tana tattauna wa da hukumomin Afghanistan don samar da yanayi mai kyau ga masu neman biza.''

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

A Afghanistan dai wacce ƙasa ce ta Musulmai, yawanci a kan yi layin maza daban da na mata ne a irin wannan lamari.

Ana kuma zaton wasu matan da tsofaffi sun ji rauni sosai.

bbc map
1px transparent line

Duk shekara ƴan Afghanistan da dama kan je Pakistan don ziyartar ƴan uwa ko zuwa asibiti ko neman aiki ko guje wa rikicin da ake yi a ƙasar.

Ofishin jakadancin Pakistan da ke yankin Nangarhar, ta bai wa mutane umarnin zuwa filin wasan ne don neman bizar saboda sun yi tsammanin mutane za su yi yawa saboda daɗewar da aka yi ba a bayarwa.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mai magana da yawun gwamnan yankin Attaullah Khogyani ya ce, ''cikin rashin sa'a a wannan safiyar dubun-dubatar mutane sun je filin wasan, abin da ya jawo wannan mummunan lamari.''