Bidiyo: Matan da ke yaƙi da al'adar da ke goyon bayan masu fyaɗe

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Matan da ke yaƙi da al'adar da ke goyon bayan masu fyaɗe
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Cin zarafin mata ta hanyar lalata ya zama ruwan dare a Pakistan. Amma shari'ar ya haifar da zanga-zanga a manyan biranen ƙasar.

Lamarin abin tsoro ne, inda ƴan fashi suka yi wa wata mata taron dangi suka yi mata fyaɗe a gaban ƴayanta, lokacin da motarta ta tsaya kan hanya.

Amma martanin da ya biyo baya ya fi tayar da barazana.

Wani babban jami'in ƴan sanda wanda ake ɗora wa alhakin gano maharan, ya ɗora laifin ga matar da aka yi ci zarafinta saboda yadda ta fito da dare ita kaɗai.

Waɗannan matan sun bayyana yadda irin wannan ɗora laifin ya zama guba da ya kamata a kawo ƙarshensa.