Nigeria: Muhimman abubuwa biyar da suka faru a makon jiya
A wannan makon ma BBC Hausa ta tsakuro wasu daga cikin labaran da suka shahara a makon da ya gabata a Najeriya tun daga 6 ga watan Satumba zuwa 12 ga wata.
Yajin aikin likitocin Najeriya

Asalin hoton, BRYAN CHRISTENSEN
A ranar Litinin na makon da ya gabata ne likitoci masu neman ƙwarewa Najeriya suka fantsama yajin aiki sakamakon zargin da suke yi na ƙin biyansu haƙƙoƙinsu da gwamnatin tarayyar ƙasar ta ƙi yi.
Likitocin dai sun koka ne kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu musamman alawus-alawus na haɗarin aiki a lokacin cutar korona.
Sai dai a ranar Alhamis likitocin suka mayar da wuƙarsu kube inda suka koma aiki, kuma hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan ministan lafiya na ƙasar Osagie Ehanire ya shaida wa likitocin cewa dole ne su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya, kuma a cewarsa, bai dace likitocin su tafi wannan yajin aikin a daidai irin wannan lokaci ba.
Ko a watan Yunin wannan shekarar ma sai da likitocin suka tsunduma irin wannan yajin aiki.
Zanen barkwancin da Bulama ya yi kan auren Hanan Buhari ya jawo ce-ce-ku-ce
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani zanen barkwanci da fitaccen mai zanen nan na Najeriya, Mustapha Bulama, ya yi kan bikin Hanan Buhai ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta inda wasu suka ce sun ji daɗin zanen wasu kuma suka nuna ɓacin ransu.
Cikin waɗanda suka nuna ɓacin ransu har da mahaifiyar amarya, wato Aisha Buhari kuma uwargidan shugaban ƙasar inda ta ce mai zanen bai yi wa bikin 'yarta adalci ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Mai magana da yawun Aisha, Aliyu Abdullahi ya shaida wa BBC cewa ƴaƴan kowanne shugaba na da damar aure idan lokaci ya zo ko da ƴan kasa na jin daɗin mulkinsu ko akasin haka.
"Zanen barkwancin Mustapha Bulama da ke yawo babu adalci a ciki saboda bikin ba shi da wata alaƙa da yanayin da yan kasa suka tsinci kansu, kuma saboda irin haka ne ya sa wata guda kafin bikin, shugabar tawa ta tattauna da ma'aikatanta cewa ba ta son a yayata bikin saboda za a taƙaita hidima," inji shi.
'Sai talakawan Najeriya sun tara min dubu ɗai-ɗai kafin na sake yi wa Buhari waƙa'

A makon da ya gabata ne fitaccen mawaƙin siyasa nan na Hausa Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya waƙa, ya ce ba zai sake yi masa waƙa ba sai an biya shi.
Rarara ya shaida wa BBC cewa zai sake yi wa Shugaba Buhari waka ne kawai idan talakawan da suka zaɓe shi kowannensu ya mika masa ₦1000.
"Talakawa masoya Buhari na ainihi waɗanda kuma akwai su, su ne za su ba ni naira dubu ɗai-ɗai sannan zan yi wa Buhari waƙa," in ji mawakin.
Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon yadda ake yaɗa jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Shugaba Buhari ya gaza a mulkinsa shi ya sa ya ce ba zai sake yin waƙa don talakawa su ji daɗi ba sai sun biya kudi.
'Yan majalisa a Kaduna sun amince da hukuncin dandaƙa ga wanda ya yi fyaɗe

Asalin hoton, FACEBOOK/KADUNA STATE GOVERMENT
'Yan majalisar jihar Kaduna sun amince da hukuncin dandaƙa ga duk wanda aka samu da laifin yin fyaɗe ga yarinya da ke ƙasa da shekara 14.
Kafin hukuncin da suka amince da shi ya zama doka har sai gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya saka hannu a kai.
Ko a kwanakin baya sai da gwamnan jihar ya fito fili ya nuna amincewarsa kan batun na dandaƙa.
Batun fyaɗe a jihohin Najeriya na daga cikin abubuwan da ake ƙoƙarin yaƙi da shi inda aka sha samun lamuran yi wa ƙananan yara fyaɗe, har ma jarirai ba su tsira ba.
'Yan bindiga sun sace mutane a Abuja

Asalin hoton, FCTA/TWITTER
A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya Abuja ta ce tana ƙoƙarin kuɓutar da mutum biyar da wasu 'yan bindiga suka sace a yankin Gwagwalada.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan babban birnin, Anjuguri Manza, ya shaida wa BBC cewa sun kuɓutar da mutum biyar daga mutanen da ƴan bindigar suka sace a ƙauyen Tungar Maje da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada.
A cewar kakakin 'yan sandan, 'yan bindigar sun tsallaka da mutane biyar ɗin zuwa cikin jihar Neja mai makwabtaka da Abuja.
Wasu mazauna garin sun shaida tabbatar wa BBC faruwar lamarin inda suka ce 'yan bindigar sun tafi da wasu daga cikinsu.










