Coronavirus a Najeriya: Wanne hatsari likitocin ƙasar suke ciki?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Peter Mwai and Christopher Giles
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
- An wallafa
Likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati sun tsunduma yajin aiki kan abin da suka kira karancin kayan aiki da biyan kudi, duk da rage cibiyoyin da ake magananin korona a cikinsu.
Ministan lafiya na kasar Dr Osagie Ehanire ya ce, yanzu an kawo karshen matsalar kayan kariyar da likitocin suke kuka a kai kuma babu ita cikin matsalolin da ake tattaunawa.
Wanne irin hadari ma'aikatan lafiyar Najeriya ke ciki?
Kungiyar likitocin masu neman kwarewar aiki ta NARD ta nuna damuwa kan adadin mambobinta da suka kamu da cutar da kuma wadanda suka mutu.
Ta ce likitocin 10 ne suka rasa rayukansu.
Tsohon shugaban kungiyar Dr Olusegun Olaopa ya ce "Tabbas mun rasa likitoci masu yawa lokacin wannan annoba."
Ana samun karin wasu likitocin da suka kamu da cutar korona a Najeriya sama da ko wacce kasar a nahiyar, ban da Afrika Ta Kudu.
Amma sun gabatar da cewa kashi 6 ne cikin 100 na rahotannin masu kamuwa da cutar a kasar, yayin da makwabciyar kasar Nijar keda kashi 19 cikin 100 wanda shi ne adadin mafi yawa a Afrika.
Sai kuma Liberia da Sierra Leon da ke biye wa Nijar din da kaso 12 cikin 100 na adadin masu cutar.
Duka wadannan kasashen da ke yammacin Afrika na da karancin masu cutar sama da makwabciyar tasu da ta fi girma a yankin, Najeriya.
Bambancin yadda kasashen ke tunkarar gwajin da kuma bayyana masu cutar ya sa ya zama abu mai wahala a kwatanta su.
Sai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, ma'aikatan lafiya a fadin nahiyar na cikin gagarumin hadarin kamuwa da cutar Covid-19.
Kasashe da dama a fadin duniya na ta fadin tashin ganin sun samar da isassun kayan kariya ga ma'aikatan lafiyarsu.

Asalin hoton, Getty Images
Matalautan kasashe ne suka fi fama da wannan karancin kayan aikin, kamar yadda cibiyar ci gaban kasashe ta duniya ta bayyana CGD.
Amma akwai wata damuwa guda daya a Najeriya, ita ce da yawa suna da yakinin babu wanda ya san nisan yaduwar cutar a kasar.
Misali a arewacin kasar a jihar Kano, an ta samun rahotanni mabanbanta kan yawan mace-macen da aka yi ta samu wadanda ake zargin suna da alaka da cutar ta korona, sai dai babu wani gwaji da ake yi.

Asalin hoton, Getty Images
Tsarin kiwon lafiyar Najeriya ya dade yana fama da karancin kudi.
An kuma ta fama da yajin aiki kan kin biyan ma'aikatan lafiyar hakkolinsu da kuma yanayin da suke aiki a ciki.
Kashi 4 cikin 100 ne kawai gwamnati ke warewa cikin kasafin kudinta game da abin da ya shafi lafiya.
A 2001, kungiyar kasashen Afrika ta roki a rika ware abin da yakai kaso 15 cikin 100 ga bangaren lafiya.
A bayan nan gwamnatin Najeriya ta nemi ta a rage kaso 43 cikin 100 na kasafin kudin samar da lafiya a matakin farko, saboda matsalar da tattalin arziki ya samu dalilin dokatr kulle da aka sanya domin shawo kan cutar da kuma faduwar farashin mai a duniya.
"Akwai karancin asibitoci da gadade a sibitocin gwamnati da rashin kudi dan haka ba za su taba aiki yadda ake bukata ba," in ji Onyeka Onwuegbunam, wani dan Najeriya kwararre a bangaren kiwon lafiya da ke jami'ar Landan.
"Tsarin kiwon lafiya a matakin farko da likitocin da kuma bangaren masu hada magunguna ba sa aikin da ya dace - haka zalika manyan asibitoci wadanda suke karbar adadi mai yawa na mutane.














