Coronavirus: Rashin zuwa makaranta ‘ya fi cutar korona illa ga dalibai – Whitty

Matakai kamar wanke jhannu da yin nesa-nesa da juna za su iya rage haɗsarin kamuwa da korona, in ji Farfesa Whitty

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Matakai kamar wanke hannu da yin nesa-nesa da juna za su iya rage haɗarin kamuwa da korona, in ji Farfesa Whitty
An wallafa

Ƙananan yara za su fi shiga haɗarin cutuwa a kan hanyarsu ta komawa gida daga makaranta a wata mai zuwa fiye da illar da cutar korona za ta yi musu idan suka kamu da ita, a cewar babban mai bayar da shawara kan harkar lafiya a Birtaniya.

Farfesa Chris Whitty ya ce "yiwuwar mutuwar yara ta hanyar korona ba wata mai yawa ba ce - amma rashin yi musu darasi "na ɓata rayuwar yaro ta lokaci mai tsawo".

Miliyoyin yara ne ake sa ran za su koma makaranta a Ingila da Wales da Ireland ta Arewa a 'yan makonni masu zuwa.

Farfesa Whitty ya kuma bayyana cewa korona za ta ci gaba da zama ƙarfen ƙafa a cikin wata tara masu zuwa.

Gwamnati ta ce ana sa ran dukkanin ɗalibai za su koma azuzuwansu don ɗaukar cikakkun darusa nan da watan Satumba.

Bayanan nasa na zuwa ne yayin da shugaban da kuma mataimakinsa ke cewa "babu wani zaɓi maras haɗari" sannan kuma yana da muhimmanci iyaye su san amfani da kuma haɗarin sake buɗe makarantu.

Wani ɗan majalisar ministocin Birtaniya ya ce za a buɗe makarantun cikin ƙwarin gwiwa idan Sashen Ilimi ya bayar da cikakkun bayanai ga iyaye da malamansu.

Saƙo ga iyaye

Farfesa Whitty ya yi amfani da tattaunawar tasa wurin shaida wa iyaye akwai hujjoji da ke nuna cewa idan yara ba sa zuwa makaranta sun fi shiga haɗarin kamuwa da "lalurar ƙwaƙwalwa da kuma ta jikinsu a cikin lokaci".

Ya ƙara da cewa akasarin yaran da suka mutu sakamkon korona suna da wasu cutukan na daban "masu tsanani".

Alƙaluma daga ofishin Hukumar Ƙididdiga na Birtaniya sun nuna cewa an samu mutuwar mutum 10 saboda korona a tsakanin 'yan shekara 19 zuwa ƙasa a Ingila da yankin Wales tsakanin watan Maris zuwa Yuni - an samu mutuwar 46,725 tsakanin 'yan shekara 20 zuwa sama.

Daga cikin yara 'yan makaranta fiye da miliyan ɗaya da suka shiga makarantun rainon yara da kuma firamare a Ingila a watan Yuni, guda 70 da kuma ma'aikata 128 ne suka kamu da cutar.