Jarrabawar WAEC: Yadda dalibai suke farin cikin bude makarantu a Najeriya
An wallafa
A ranar Talata ne aka sake bude makarantu a wasu yankunan Najeriya bayan da aka rufe su wata da watanni sakamakon annobar korona.
Gwamnatin kasar ta ce ta sake bude makarantun ne ga 'yan ajin karshe musamman masu shirin rubuta jarrabawar sakandare ta WAEC.
Mun tataro ra'ayoyin wasu daga cikin dalibai kan sake bude makarantun: