An ga Buhari da takunkumi, Dogara ya koma APC: Abubuwan da suka ja hankali a Najeriya makon jiya

An wallafa

Suman da shugaban hukumar NDDC ya yi ana tsaka da jin bahasi na bincike kan zargin almubazzanci da komawar tsohon kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara zuwa jam'iyyar APC na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a makon da muke ban kwana da shi.

Mun duba muku manya daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya kamar haka:

Shugaban NDDC ya sume ana tsaka da bincike

Daniel Pondei

Asalin hoton, Others

A ranar farko ta wannan makon ne Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya sume yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi.

Lamarin ya faru ne yayin da Daniel Pondei yake bayar da bayani ga 'Yan Kwamitin Majalisar Tarayya kan Neja Delta kan yadda hukumar ta kashe sama da naira biliyan 40 cikin wata uku.

Numfashin Pondei ya ɗauke kuma ya sunkuyar da kai jagab a kan kujerar da yake zaune, a ƙarshe sai fitar da shi aka yi daga ɗakin taron.

Bisa wannan dalili ne shugaban kwamitin ya ba da sanarwar tafiya hutun minti 30.

Yakubu Dogara ya koma jam'iyyar APC

Buhari da Yakubu Dogara da Mai Mala Buni

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya bar jam'iyyar adawa ta PDP inda ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

A ranar Juma'a ne, Gwamnan Yobe Mai Mala Buni ya yi wa Yakubu Dogara jagoranci zuwa wajen Shugaba Muahammdau Buhari a fadarsa da ke Abuja.

Mai Mala wanda shi ne shugaban kwamitin musamman da ke aikin sasanta 'ya'yan jam'iyyar, ya ce yanzu an sasanta game da dalilin da ya sa Dogara ya bar APC tun farko.

Dogara bai ce wa 'yan jarida komai ba, yana mai cewa zai yi magana kan batun a nan gaba.

Ministan yankin Neja-Delta ya yi amai ya lashe

Godswill Akpabio

Asalin hoton, Channels TV

Ministan ma'aikatar kula da yankin Neja-Delta, Godswill Akpabio ya ce ba a fahimce shi ba game da maganar da ya yi cewa akasarin kwangilolin da hukumar NDDC ta bayar 'yan majalisar tarayya aka bai wa.

Wannan ya biyo bayan wa'adin da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabeamila ya ba shi, na ya wallafa sunayen 'yan majalisar cikin sa'a 48 ko kuma su ɗauki mataki a kansa.

Cikin wasiƙar da ya tura wa majalisar a ranar Alhamis, Akpabio ya ce bai ce an bai wa 'yan majalisar kashi 60 cikin 100 na kwangiloli ba, kamar yadda aka riƙ ruwaitowa.

Jinkirin da aka samu gabanin isar wasikar ya sa kakakin majalisar ya umurci Akawun Majalisar da ya bi matakan da suka dace don gurfanar da ministan a gaban kotu bisa tuhumarsa da yin ƙarya da ɓata sunan 'yan majalisar.

Boko Haram ta kashe ma'aikatan agaji biyar a Borno

A ranar Alhamis ne aka samu rahotannin kashe ma'aikatan agaji guda biyar a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Mutanen suna aiki ne da ƙungiyoyin Action Against Hunger da International Rescue Committee da Rich International da kuma State Emergency Management Agency.

Shugaba Muhammadu Buhari ya zargi ƙungiyar Boko Haram da aikata kisan sannan ya sha alwashin gurfanar da waɗanda suka aikata a gaban kotu.

An ga Shugaba Buhari da takunkumi a bainar jama'a karon farko

Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

A karon farko ranar Alhamis, an ga Shugaba Buhari da takunkumin kariya daga cutar korona a bainar jama'a yayin da ya isa ƙasar Mali.

Tafiyar shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda ke daga cikin masu shiga tsakani na ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin sasanta rikicin siyasa.

Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irinsu Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su haɗu a Mali domin tattaunawa don yin sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma 'yan adawar ƙasar.