An kwantar da Sarki Salman na Saudiyya a asibiti

An kwantar da sarki Salman Bn Abdul'aziz na Saudiyya a wani asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje.
Bayanai sun ce Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara.
Da safiyar yau Litinin ne Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ruwaito cewa an kwantar da Sarki Salman asibitin na Riyadh ba tare da wani cikakken bayani ba.
Amma Kotun Masarautar Saudiyya ta ce mafistararsa ce ta kumbura kuma ana ci gaba da bincike.
Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya - kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012.
Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin gwamnan Riyadh.
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, ya bayyana cewa Firaministan Iraki Mustafa Al-Kazemi, ya dage ziyarar da ya shirya kai wa Saudiyya.
Labarin rashin lafiyar Sarki Salman Yanzu ya sa hankali ya karkata ga makomar Saudiyya musamman zamanin Muhammad Bin Salman, Yarima mai jiran gado wanda tuni ake ganin shi ke tafiyar da jagorancin Saudiyya.
Yariman mai jiran gado shi ya kaddamar da sabbin sauye sauye na tattalin arziki na kokarin karkatar da dogaro da kasar Saudiyya ke yi da arzikin feitr.
Wannan ya sa Yariman mai shekara 34 ya samu karbuwa da goyon baya musamman tsakanin matasan Saudiyya na kawo wasu sabbin abubuwan da ba a taba gani ba a kasar musamman ba mata 'yanci.
Amma wasu na bayyana damuwa kan nuna karfi iko akan kafofin watsa labarai da kuma kama-karya da aka gani.











