Kamfanonin maganin jabu na cin karensu babu babbaka a Yammacin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Abu ne mai wuya a Najeriya ka ji ana tattauna matsalar magunguna na bogi ba tare da maganar abin takaicin nan na maganin "My Pikin" ba.
Harkar samar da magunguna na jabu sai bunƙasa ta ke yi a yankin Afirka ta Yamma, duk da kokarin da hukumomi ke yi na kawar da masu aikata laifuka tare da haɗin gwuiwar manyan kungiyoyin da ke samar da magungunan daga ƙasashen waje.
A 2009, yara 84 aka kashe bayan da suka sha wani maganin fitar haƙori da ke ɗauke da sinadarin diethylene glycol, wanda ake amfani da shi wajen haɗa sinadarin tsafatace kaya da birkin mota.
Wata kotu ta kama wasu ma'aikata biyu na kamfanin da ya haɗa maganin da laifi.
Magungunan bogi
Shari'ar na da muhimmanci domin sayarwa da haɗa magunguna na jabu abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya.
"An yi sa'a wannan labarin ya kai ga kunnuwan jama'a," in ji Likita Alero Roberts, inda ta kara da cewa: "Muna da matsaloli masu yawa."
Likita Roberts babbar malamar Asibitin Koyarwa na Jami'ar Legas ce, kuma ta yi sa'a cewa asibitin na da ingantaccen tsarin sayen magaunguna kuma ba a fuskantar matsalar magunguna na jabu, amma ana ganin marasa lafiya da suka fada cikin matsalar shan magunguna na bogi.

Asalin hoton, Getty Images
Ta kuma damu cewa matsalar za ta ƙaru a watanni masu zuwa saboda tasirin da cutar korona ke da shi kan samar da magunguna a Najeriya.
"Akwai yiwuwar za a sami ƙarancin magunguna - na cutar daji da masu inganta kariyar jiki," inji Dokta Roberts.
Idan babu magani a dakunan samar da magani na asibitoci marasa lafiya kan tafi wasu wurare domin sayo su, kuma akasari suna samunsu ne daga kasuwannin da babu mai sa ido a kansu.
Ba kuma sai an yi nisan kiwo ba, domin daga tagar ofishin Dokta Roberts, tana iya hango ƴan kasuwa na sayar da abu biyu - "magunguna da akwatunan gawa".
Ba sabon abu ba ne ka ga ƴan kasuwan na sayar da magunguna bisa tituna a Afirka ta Yamma - inda cinikin magunguna ya zama kasuwanci ne ba sana'a ba.
More than 30 million counterfeit tablets shipped from India were seized in one week in Lagos"

Rashin sa ido daga hukumomi shi ne ɗaya daga cikin matsalolin da ke sa kungiyoyin masu aikata laifuka ke ƙara yawa cikin harkar samar da magunguna na jabu. A Afirka ta Yamma, cinikin magunguna babban abu ne.
Baragurbin da ke haɗa magunguna na jabu na ba Mohammed Babandede ciwon kai. Babandede shi ne shugaban bangaren da ke kula da ingancin kayayyakin da ke shiga kasar a hukumar shige da fice ta Najeriya, kuma annobar korona ta haifar da wata sabuwar matsalar magunguna na jabu.
"Abin da ban tsoro," inji shi, kuma ya ce a mako guda sun taɓa kama kwayoyin magani na jabu fiye da miliyan 30.
Ya kuma ce hukumomin Indiya ne suka sanar da su cewa za a shiga da wasu magunguna na jabu cikin kasar ta tashar jirgin ruwa na Tin Can Island da ke Legas.
Cikin kayan da suka kama akwai magann dexamethasone na jabu - wanda amagani ne da ake amfani da shi wajen warkar wasu alamomi na cutar korona.
A cikin wannan makon kuma ya kama kwayoyin tramadol na jabu a filin jirgin sama na Legas da aka shiga da shi kasar daga Mumbai, babban birnin kasar Indiya. Kafin a kama su, magunguna na kan hanyarsu ta zuwa kasuwannin arewacin najeriya ne inda shan kwaya ya zama ruwan dare gama duniya.

Babandede ya kuma ce kama masu shigo da magungunan na jabu ba da wahala saboda a kan boye ainihin inda za a kai su da kuma inda suka fito - saboda haka hukumomi ba sa iya gano waɗanda suka shigar da magungunan ciki ƙasar.
Adebayo Alonge na cikin waɗanda magunguna na jabu suka yi wa illa.
Ya taba sayen salbutamol a 2003 daga wani shagon sayar da maani a Ibadan da ke kudu maso yammacin Najeriya.
An sauya ainihin sunan da ke jikin maganin, kuma an zuba sinadarin diazepam mai yawa, wanda ya somar da shi na tsawon mako uku.

Asalin hoton, Getty Images
Batu ne na a mutu ko a yi rai
Rashin kayan aiki na daƙile ayyukan hukumomin da ake sa ido kan shige da fice a iyakokin yankin Afirka ta Yamma.
"Muna ƙara faɗaɗa ayyukanmu, muna mayar da hankali kan wuraren da aka fi shigar da magunguna domin daƙile yunkurin masu aikata laifi."
Ana kiyasta mutum 116,000 na rasa rayukansu a kowace shekara saboda shan magungunan jabu da suka yi a yankin Afirka ta Yama kawai, saboda haka wannan ƙoƙarin na iya zama na a mutu ko a yi rai.











