Dexamethasone: An tabbatar tsohon maganin yana warkar da cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
Masana kiwon lafiya sun bayyana Dexamethasone, wani magani mai saukin kudi, wanda kuma aka dade da saninsa a matsayin abin aka dade ana nema wajen magance masu tsananin fama da cutar Covid-19.
Masu bincike a jami'ar Oxford sun gano maganin na inganta damar da masu cutar ke da ita na warkewa cikin hanzari, musamman idan har ta kai ga sai ana mu su karin iska, ko ana taimaka mu su su yi numfashi da na'ura.
Masu binciken sun lura cewa maganin mai suna Dexamethasone kan rage kashi daya cikin uku na yawan masu mutuwa daga cutar idan har ana mu su karin iska ne.
Binciken da aka gudanar a jami'ar Oxford ta Ingila ya nuna cewa maganin kan sa garkuwar jiki mayar da martanin da ya dace idan cutar korona ta bayyana a jikin dan Adam.
Daya daga cikin masu binciken, Professor Martin Landray na Sashen Ilimin Kiwon Lafiyar Al'umma a Jami'ar ta Oxford ya ce sakamakon da suka samu daga gwajin maganin ya ba su mamaki:
"Lokacin da muka fara lura da sakamakon, mun yi mamaki domin ya zarce dukkan abin da muka sa ran gani."
"Ganin irin wannan sakamako mai karfafa gwuiwa a jikin wadanda cutar ta durkusar ya katimaka ma na wajen ci gaba da neman maganin cutar - duk da cewa muna ta neman abin da tuni muka sani," inji shi.
Ya kuma ce Dexamethasone magani ne mai saukin samu, wanda kuma ba shi da tsada, saboda haka sakamako ne mai dadin ji.
Sai dai tilas ne a ci gaba da neman wani maganin domin Dexamethasone ba zai warkar da dukkan masu fama da cutar ba.
Na farko ba zai dace da kowane irin nau'i na wadanda ke dauke da cutar ba.
Amma abu ne mai karfafa gwuiwa idan aka tuna cewa a makon jiya-jiyan nan bamu da magani ko daya da za mu iya dogara da shi wajen yaki da wannan annoba.











