Coronavirus: Mene ne dexamethasone kuma ta yaya zai magance Covid-19?

Asalin hoton, Getty Images
Wani maganin kumburi mai sun dexamethasone ya ciri tuta a matsayin wanda ake amfani da shi ga masu dauke da cutar covid-19 dake jinya a asibiti.
Wani gwaji da aka yi a Birtaniya ya nuna cewa maganin zai iya ceto rayuka, kuma tuni aka ba da damar asibitoci a kasar su fara amfani da shi ba tare da bata lokaci ba.
Wane magani ne?
Dexamethasone wani magani ne dake sace kumburi, inda yake tsotse kwayoyin halittar dake kumbura jiki.
Ta ya yake aiki?
Wannan maganin yana aiki ne ta hanyar rage karfin garkuwar jiki.
Cutar korona tana haifar da kumburi (a huhun mutum) yayin da jiki yake kokarin yakar cutar.
Amma a wasu lokutan garkuwar jikin tana aiki fiye da kima, kuma wannan ne ke haifar da illa - martanin da ya kamata ya yaki cuta, sai kuma ya kare yana yakar kwayoyin halittar jikin mutum.
To shi maganin dexamethasone yana rage karfin wannan tasirin ne.
Maganin ya fi dacewa a yi amfani da shi ne ga mutanen da suke a asibiti, kuma ake yi musu amfani da na'urar taimakawa wajen numfashi - ma'ana mutanen dake cikin mawuyacin hali.
Sai dai ba ya amfani ga mutanen da koron ba ta yi wa mummunan kamu ba, kuma ragewa garkuwar jikinsu karfi a wannan mataki ba zai taimaka musu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ya tasirin maganin yake?
A cewar masana kimiyyar da suka gudanar da binciken, maganin zai iya taimakawa wajen ceto ran mutum daya daga cikin uku da aka sakawa na'urar taimakawa wajen numfashi.
Wadanda ta kai ga an saka musu iskar oxygyn kuwa, magananin zai iya taimakawa wajen ceto ran mutum daya daga cikin biyar.
Babu wani alfanu na azo a gani da maganin zai yi ga wadanda ba sa bukatar tallafin wajen numfashi.
Ya aka gudanar da binciken?
An samu sakamakon ne daga gwajin da aka yi a jinyar masu fama da cutar korona, wanda Jami'ar Oxford ta gudanar.
An yi gwajin ne don gano ko magunguna da ake amfani da su kan wasu cutukan za su yi amfani wajen jiyar masu fama da cutar korona.
An riga ba wa mutum 2,100 maganin 6mg na dexamethasone a kullum har tsawon kwana goma.
An gwada ci gaban da suka samu da yanayin wasu mutum 4,300 wadanda ba a yi musu wata jinya ta musamman ba.
Masana kimiyya sun yi fatan cewa za a iya amfani da dexamethasone a cikin jerin magungunan da za su iya rage hadarin mutuwa.
A yanzu an bada shawarar cewa a ringa ba wa manya maganin, amma ban da mata masu ciki da masu shayarwa.
Ya saukin samuar maganin?
Maganin dexamethasone yana da araha, wanda kuma ake samunsa ko ina kuma cikin inganci.
Gwamnati ta ce tuni ta tanadi maganain da za a iya yiwa mutum 200,000 jinya da shi, a lokacin da ake fatan samun kyakkyawan sakamako daga gwajin.
A Birtaniya ana maganin da mutum zai sha rana daya yana kaiwa £5.40 (kwatankwacin Naira 2,597), kuma za a sha shi ne tsawon kwana goma.
An fara yin maganin ne a 1957 sannan ya zama gama gari a Birtaniya a farkon shekarun 1960.
Saboda dadewar maganin, babu hakkin mallaka a kansa.
Hakan na nufin cewa kamfanoni da dama za su iya yin sa, kuma a fadin duniya ma maganin ya yadu sosai.
Wannan labari ne mai dadi musamman ga kasashe masu tasowa, kuma hukumar lafiya ta duniya ma ta yi maraba da gwajin.

Asalin hoton, JUSTIN TALLIS/AFP
Wadane cutuka kuma ake jiya da maganin?
Maganin zai taimaka wajen jiyar cutuka da dama, da suka hada da kumburi a jiki, ko kuma yanayin da zai sa garkuwar jiki ta yi aiki fiye da kima, kamar ciwon asma, wacce za ta iya janyo hanyoyin numfashi su toshe ku kma huhu ya kumbura, da masu fama da yawan laulayi, ko kuma kumburin gabobi.
Ko maganin yana da wata illa?
Illolin maganin dexamethasone sanannu sun hada da damuwa, da karancin bacci, da kara kiba.
Wasu illolin da ba a iya gani ba sun hada da ciwon ido, da gani garara-garara da futar jini daga jiki.
To sai dai masu fama da cutar korona suna bukatar maganin ne kadan, wanda hakan zai takaita illar sa.
Babban daraktan lafiya na yankin Ingila ya ce "babu wata illar azo-a-gani da aka gani wajen amfani da maganin na dexamethasone a marasa lafiyar dake Ingila.













