Ghana za ta sake gina ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra

An wallafa

Ministar harkokin wajen Ghana ta ce kasarsa za ta sake gina ofishin jakadancin Najeriya da ke Accra wanda aka rusa.

A makon da ya wuce ne wasu mutane dauke da makamai suka lalata ginin wanda ba a kammalashi ba.

Tuni aka damke mutane biyu bisa zargin wannan aika-aikar.

Ministar harkokin wajen, Shirley Ayorkor Botchwey ta ce gwamnati za ta gaggauta gyara wuraren da aka rusa a ginin.

Ta ce za a kuma bai wa ofishin jakadancin Najeriya cikakkun takardun filin.

Ms Botchwey ta kara da cewa Ghana za ta ci gaba da aiki domin tabbatar da cewa an kare ma'aikatan jakadancin a cikin kasar.

A cewarta gwamnatinsu na tattaunawa da Najeriya domin warware matsalar.

A ranar Litinin, 'yan Najeriya mazauna Ghana sun yi zanga-zanga kan rusa ginin.