Coronavirus a Kano: Ƙarin mutum 23 sun kamu, 2 sun mutu

Gwamna Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, KNSG

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ma'ikatar lafiya ta Kano a Najeriya ta ce an sake samun mutum 23 da suka harbu da korona a rana guda a jihar.

Jadawalin alkaluman da ma'aikatar ta fitar ya ce akwai mutum 134 da suka warke sarai, sannan an samu karin mutum 2 da suka mutu wanda hakan ya kawo adadin mamata a jimlace 38.

Alkaluman daren Litinin ya kuma nuna cewa yanzu mutum 747 ke kwance a cibiyar killace masu dauke da wannan cuta.

Jihar Kano da ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya, yawan masu cutar da wannan sabon adadi yanzu ya kai 919.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

BBC
Karin bayani kan coronavirus

Jadawalin jiha 34 da birnin Abuja da cutar ta bulla ya nuna Kano ce har yanzu ta biyu a yawan masu cutar korona da mutum 919, a bayan Legas mai mutum 3,595.

Al'ummar Kano dai na dakon ranar cire musu dokar kulle da aka sake tsawaita ta da mako biyu gab da lokacin shirye-shiryen sallah.

Koda yake gwamnatin jihar ta sassauta dokar inda aka bada damar Sallar Idi da kuma cigaba da gudanar da Juma'a

Bikin Sallah bana ba ta zowa al'ummar Najeriya musamman na arewaci da dadi ba ganin yadda annoba ta kassara shagulgula.

Masana dai sun yi ta bayani da gargadi kan yi takatsantsan da samun karuwar annobar, yayinda jihohi ke daukan matakan sassauta dokar kulle.

Jihohi irinsu Jigawa da Borno tuni suka dage dokar kulle inda suka bai wa mutane damar halartar sallolin jam'i.

Ita ma ana ta bangaren gwamnatin Tarayya ta gargadi gwamnoni da neman hadin-kai wajen yaki da wannan annoba.