Ko maganin Maleriya da Trump ke sha na maganin cutar korona?

Trump

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana shan maganin maleriya na hydroxychloroquine domin kashe kwayar cutar korona duk da cewa jami'an lafiya na gargadi da yin hakan.

Da yake magana a fadar White House, mista Trump ya shaida wa manema labarai cewa ya fara shan maganin a baya-bayan nan.

"Na kimanin mako guda ina shan maganin kuma gani kyam, gani lafiya lau." ya fada cike da mamaki.

Mr Trump dai ya fara gwajin maganin maleriyar ne a watan Maris inda ya janyo maganin ya yi tashin gwauron zabbi a Amurka.

To sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce babu wata kwakkwarar sheda da ke nuna maganin na samar da waraka ga cutar korona, inda ta yi gargadin cewa jama'a su guji zaman likitan kansu domin hakan na da illa ga lafiyarsu.

Ita ma Hukumar Tabbatar da Ingancin Magunguna ta Duniya, FDA ta yi gargadi a watan Afrilu cewa maganin na gada cutuka masu alaka da zuciya sannan ta shawarci jama'a da su guji amfani da shi.

Kasashe dai da dama na gudanar da bincike da nazarce-nazarce kan ingancin da maganin na maleriya yake da shi wajen kashe kwayar cutar korona.

Shugaba Trump na Amurka dai ba ya dauke da cutar, amma kasarsa ce a gaba-gaba wajen yawan masu ita, al'amarin da ya sa ya kasa zaune ya kasa tsugune.