Mahaifa sun yi tozali da ɗansu da aka sace bayan shekara 30

China

Asalin hoton, CCTV

An wallafa

Wani miji da matarsa da aka yi garkuwa da dansu a dakin otal a 1988 sun yi tozali da dan nasu bayan shekaru 32.

An dauke Mao ne yana dan shekara biyu a lokacin da mahaifinsa ya tsaya neman ruwa a kan hanyarsa ta komawa gida daga lambunsa.

Mahaifan nasa dai sun ta faman neman dan nasu inda suka raba takardun da ke dauke da hotonsa har guda 100,000.

Iyayen sun yi tozali da dan nasu ne a ofishin 'yan sanda ranar Litinin kuma dan nasu wanda yanzu ya kai shekara 32 ya yanke shawarar zai zauna da mahaifan nasa na dan wani lokaci.

Me ya faru da Mao Mao Yin?

An dai haifi Mao ranar 23 ga watan fabrairu 1986. A wata hira da jaridar China a watan Janairu kafin a gano shi, mahaifiyarsa ya bayyana shi da mutum mai wayo.

A ranar 17 ga watan Oktoba 1988, yaron tare da mahaifinsa Mao Zhenjing na tafiya gida bayan zuwa lambu sai yaron ya tambayi mahaifin nasa inda zai samu ruwa ya sha.

Hakan ne kuma ya sa mahaifin da dan nasa suka dakata a kusa da wani otal, inda Zhenjing ya dafa ruwan da zai bai wa Mao to amma sai ya duba bai gan shi ba. An dauke Mao.