Coronavirus ta harbi mutum 5,641 a Najeriya, 1,472 sun warke

Asalin hoton, Getty Images
Sabbin alkaluma da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya ta fitar a daren Asabar sun nuna cewa masu dauke da korona yanzu haka a kasar sun kai 5,641.
Wannan ya biyo bayan samun karin mutum 176 da suka sake kamuwa da cutar korona a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Yanzu dai adadin mutane da cutar ta hallaka a fadin kasar ya kai 176, yayinda mutum 1,472 suka warke.
A Legas, jihar da ta fi yawan masu fama da korona, sabbin alkaluma sun nuna an sake samun mutum 95 da suka kamu.
A jihar Oyo an samu mutum 31, birnin Tarayya Abuja ke mataki na Uku a jadawalin daren Asabar da mutum 11 sabbin kamu.
Jihar Neja na da mutum 8, haka ma a Borno mutum 8, inda jihohin Jigawa 6 Kaduna kuma 4.
Haka kuma, mutum 3 sun sake kamuwa da cutar a Anambra, Edo da Ribas da Nasarawa da Bauchi kowanne na da mutum biyu-biyu.
Sai kuma Benue da Zamfara da ke da mutum guda kowanne.
Jihar Kano a wannan lokaci ba a samu mutum ko daya da ya kamu ba, sai dai an samu mutuwa 2, yayinda wasu karin mutum biyu suka warke daga cutar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X


Muhimman bayanai kan annobar korona
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.
A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.
Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.
Har yanzu a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu.
Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.
Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Asabar 15 ga watan Mayu.

Asalin hoton, @NCDCgov











