Ina nan da rai na - Shiekh Bala Lau

Bala Lau

Asalin hoton, JIBWIS

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban ƙungiyar Izala a Najeriya Shiekh Abdullahi Bala Lau ya ƙaryata labarin mutuwarsa da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa a shafinta na intanet da kuma Twitter a ranar Lahadi.

Shiekh Bala Lau ya shaida wa BBC cewa "Ina nan lafiya lau."

A labarin da ta rubuta da ya tayar da hankalin ƙungiyar Jama'atul Izalatul bid'ah wa Iqamatus Sunnah, Sahara Reporters ta ce shugaban ƙungiyar ya rasu a ranar Asabar.

Ta kuma wallafa hotonan jana'iza a shafinta na Twitter tare da hoton gawar da ta ce ta Shiekh Bala Lau ce da aka yi jana'izarsa da safiyar Lahadi.

Shafin Twitter na Sahara Reporters
Shafin Twitter na Sahara Reporters

A hirarsa da BBC, Shiekh Bala Lau ya ce "ba mu san dalilin rubuta wannan labarin ba. Ya kamata a tuntubi iyalinmu ko ƙungiyarmu ta Izala.

"Rayuwa tana da farko kuma tana da karshe kamar yadda Allah ya karbi rayuwar Annabi SAW. Amma bai kamata ace jarida ta dauki labarin da ba ya da tushe ba. Wannan wata kiyayya ce."

A nata bangaren ƙungiyar Izala bayan karyata labarin mutuwar shugabanta, ta bukaci Sahara Reporters ta fito ta gaggauta ƙaryata labarin da ta yaɗa.

Shiekh Isa Ali Pantami, ya ce hotunan da Sahara Reporters ta wallafa na jana'izar Shiekh Adam Muhammad Gashua ne, tare da shawartar kafar ta fito ta gyara.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A hotunan da Sahara ta wallafa ta ce mutane sun taru wajen jana'izar Shiekh Bala Lau inda suka yi watsi da ƙa'idar yin nesa nesa da juna da ake son mutane su yi saboda tsoron bazuwar cutar korona.

Zuwa Yanzu Sahara Reporters ba ta yi ƙarin bayani ba game da labarin da ta wallafa, ko ta nemi gafara. Ko da yake ta goge labarin da ta wallafa a Twitter.