Rashin kayan gwaji na tsaiko ga yaki da cutar korona a Lagos

Asalin hoton, Twitter
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce jihar ta dauki samfurin mutum 3,000 domin yin gwajin cutar korona amma sakamakon rashin kayan gwaji mutanen da aka dauki samfurinsu ba su san matsayinsu ba.
"Muna samfurin mutum 3,000 da muka dauka to amma ba mu samu damar yin gwajin ba saboda rashin kayan gwaji da duniya ke fama da shi. Amma muna fatan wasu kayan gwajin za su zo mana a gobe Talata."
Ya kara da cewa "mun yi odar karin kayan gwajin saboda yawan masu cutar da muka gani kuma da alama za a iya samun kaso 20 masu dauke da cutar a cikin mutum 3,000 da muka dauki samfurin nasu."
A ranar Litinin ne dai aka dage dokar kulle a jihar Legas da Ogun da kuma birnin Abuja, inda jama'a suka yi fitar farar dango domin gudanar da harkokin neman abincinsu.
To sai dai gwamnatin jihar ta Legas ta ce ta sanya dokar hana fita daga karfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe.

Har wa yau, Gwamna Sanwo-Olu ya ce ba duk ma'aikatan gwamnati ne za su koma bakin aikinsu ba, inda yanzu ma'aikatan da ke mataki na 15 zuwa sama ne za su koma bakin aiki, kafin daga bisani sauran ma'aikatan su koma aiki da sannu-sannu.
Dangane da kasuwanni kuma gwamnan ya ce kasuwannin sayar da kayan abinci za su rinka budewa a ranakun Talata da Alhamis da Asabar daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma.
Su kuma kasuwanni da ba na abinci ba za su rinka bude hajarsu ne a duk ranakun Litinin da Laraba da Juma'a daga karfe 9;00 na safe zuwa 3:00 na yamma, sannan kuma wajibi yin amfani da takunkumi da man goge datti.
Har wa yau, bankuna da kamfanoni za su yi aiki daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma a duk ranakun mako amma kaso 60 na ma'aikatansu ne za su rinka zuwa ofis.
Gwamna Sanwo-Olu ya bayar da umarnin a saki ababan hawan da aka karbe na mutanen da suka ki bin dokar kulle a jihar.











