'Yan majalisar Uganda za su amayar da kudin coronavirus da suka ci

Uganda MPs Cash Scandal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wata babbar kotu a Kampala, babban birnin kasar Uganda ta umarci 'yan majalisar kasar su mayar da kudaden da suka raba wa kansu, wadanda suka ce za su yi amfani da su domin yakar cutar korona.

Shugaba Yoweri Museveni ya bayyana matakin na 'yan majalisar a matsayin abin kyama.

Babbar kotun ta bukaci 'yan majalisar su mayar da kudaden ga akawun majalisar kasar ko kuma su mika su ga kwamitocin yankuna ko na kasa da aka kafa domin su yaki cutar korona a kasar.

Wannan lamarin dai ya samo asali ne yayin da majalisar Ugandan ta kafa dokar wani kasafin kudi na musamman domin ma'aikatar lafiya ta kasar ta sami zarafin tunkarar annobar ta korona, amma sai 'yan majalisar suka rabawa ko wane dan majlisa cikinsu dala dubu biyar-biyar.

Amma wasu tsiraru cikin 'yan majalisar sun ki karban kudin, sai dai sauran sun ce sun karbi kudin ne wai domin su tallafa wa al'umomin mazabun da suka zabe su a wannan lokaci da annobar korona ke kara bazuwa.

Kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam sun soki matakin na 'yan majalisar, inda suka ce handama da babakere ne manufarsu ba bayar da taimako ba.

Sai dai bayanai na fitowa da ke cewa wasu daga cikin 'yan majalisar tuni suka kashe kudaden.

Ma'aikatan lafiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ma'aikatan lafiya - Uganda ta sha fama da cuatr Ebola a shekarun baya

Shugaba Yoweri Museveni ya umarci ofishin babban mai shigar da kara na kasar ya binciki yadda 'yan majalisar suka kashe kudaden. Yawancin 'yan majlisar mambobin jam'iyyar NRM ta shugaban ne, wadda ita ce ke mulkin kasar.