Tsawa ta kashe wasu birai na musammana a Uganda

Asalin hoton, Getty Images
Wasu birrai guda hudu, ciki har da wata mai ciki, sun rasa rayukansu bayan aradu ta fado masu a kasar Uganda, kamar yadda wata kungiyar kiyaye namin daji ta bayyana.
Birran, wadanda jinsinsu ba shi da yawa a duniya, an gan su ne a gandun Mgahinga National Park da "raunuka a jikinsu", abin da ke nuna kamar an yi musu shokin da wutar lantarki.
Kungiyar Greater Virunga Transboundary Collaboration (GVTC) ta bayyana lamarin da cewa "babbar asara ce ga jinsinsu".
Baki daya jinsin biran da ake kira mountain gorilla 1,000 ne a raye a ban kasa.
Halittun a kebe suke tsakanin kasashen Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da Rwanda da kuma Uganda.

Asalin hoton, Getty Images
Guda hudun da suka mutu wani bangare ne na rukunin da hukumomi ke yi wa lakabi da iyalin Hirwa, su 17.
Iyalin Hirwa sun tsallako ne daga Rwanda zuwa cikin Uganda a shekarar da ta gabata, kuma sun ci gaba da zama ne a Mgahinga National Park.
"Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske," Andrew Seguya, babban sakataren kungiyar GVTC ya shaida wa BBC.
"Gudunmawar da mata hudu na cikinsu ke bayarwa ga jinsunsu muhimmiya ce."
Dr. Seguya ya kara da cewa an gano wasu 13 na iyalan Hirwa kuma suna murmurewa.











