Coronavirus: Trump ya ce wasa yake game da allurar maganin wanke datti

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce maganar da ya yi ta cewa maganin kashe kwayoyin cutuka wato disinfectants zai yi maganin cutar korona "ba'a ce yake yi".
Yayin wani taron saka hannu kan tallafin annobar korona a ranar Juma'a, Trump ya ce "yana tsokanar 'yan jarida ne kawai don ya ga me zai faru".
Amma ya kara da cewa goga maganin a hannu "zai yi tasiri sosai".
Kungiyar likitoci a Amurka ta caccaki shugaban kasar Donald Trump bayan shawarar da ya bayar kan cewa a yi bincike ko za a iya maganin cutar korona da damaganin wanke datti.
Kazalika ya kara ba da shawarar amfani da hasken kashe datti wajen maganin cutar, Shawarar da wani likita ya yi facali da ita nan take.
Kafin wannan shawarar, wani daga cikin jami'an gwamnatinsa ya bayyana cewa ana amfani da hasken rana da maganin wanke datti ne kawai wajen kashe kwayoyin cuta.
Magungunan kashe datti abubuwa ne masu cike da hadari kuma za su iya zama guba idan aka sanya su jikin dan adam.
Ko wanda ake zuba wa jikin dan adam yakan zama hadari ga fata da ido da kuma yanayin nunfashi.
Me Shuagaba Trump ya ce?
Yayin bayani kan cutar korona a fadar White House ranar Alhamis, wanda kwamitin kar-ta-kwana ke yi, wani jami'i ya gabatar da sakamakon wani bincike da gwamnatin Amurkan ta jagoranta wanda ya nuna cutar korona na rauni nan da nan a cikin hasken rana ko kuma wurin da ke da zafi.
Bincike ya kuma nuna maganin wanke datti zai iya kashe cutar ta cikin yawu ko gumi cikin dakika biyar, haka ma wani nau'in alcahol mai wari zai iya kashe ta cikin gaggawa.
Williams Bryan mai rikon kwaryar shugabancin ma'aikatar tsaron cikin gida da kimiyya da fasaha ne ya zayyana sakamakon binciken a wani taron manema labarai.
Yayin da yake ba da shawarar a bi wannan bincike cikin nutsuwa, Shugaba Trump ya kuma kara ba da shawarar ci gaba da wani binciken a dai wannan fanni.
"Idan muka zuba wa jiki wannan maganin ko kuma hasken nan mai matukar karfi" shugaban yana magana yana kallon Dakta Deborah Brix, shugabar kwamitin kar-ta-kwana, "kuma kin ce hakan da kamar wuya amma daga baya za ku gwada shi.
"Ina ganin idan muka zuba wannan haske cikin jiki, wanda na tabbatar za ku iya ta jikin fata ko kuma ta wata hanyar. Kuma kunce za ku gwada wannan ma. Hakan zai yi ma'ana," Shugaba ya ci gaba da cewa.
Yana nuna kansa,"Ni ba likita ba ne. Amma ni mutum ne da ke da kun san me."
Ya kara juya wa ya kalli Dakta Birx ya tambayeta in kin taba jin an yi amfani da "zafi da kuma haske" wajen maganin korona.
"Ina ganin abu ne mai muhimmanci da ya kamata mu nazari a kai," in ji Trump.













