'Yadda na warke daga Coronavirus a New York'
An wallafa
Ku saurari tattaunawa da BBC ta yi da wanda ya warke daga cutar korona ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke sama.
Mutane daban-daban a duniya, wadanda suka yi jinyar cutar korona suna bayani a kan irin mawuyacin halin da suka shiga.
Mallam Ibrahim Garba Ahmad wani dan Najeriya ne mazaunin birnin New York a Amurka, wanda ya tsallake rijiya da baya, bayan ya kamu da cutar.

Asalin hoton, Ibrahim Garba Ahmad
A tattaunawarsa da Ibrahim Isa, ya ce jinyar da ya yi ta sa ya kara gasgata cewa cutar korona gaskiya ce, kuma ya kamata sauran jama`a su kiyaye. Ya fara ne da bayani a kan yadda ya harbu da cutar.









