Coronavirus: An fara raba tallafin kwai a Zamfara

Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle

Asalin hoton, BELLOMATAWALLE1

An wallafa

Jihohi da dama ne dai a Najeriya da ba a samu bullar cutar korona ba suka shiga daukar matakan ko-ta-kwana ganin yadda cutar ta kai zuwa yankunann da suke ko kuma jihohin da ke makwabtaka da su.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da cutar ba ta bulla ba, amma hukumomi a jihar sun ce suna daukar matakan kariya tun yanzu, saboda mai kwarmin ido da wuri ya ke soma kuka inji mahukuntan.

Honourable Nasiru Mu'azu Magarya, shi ne kakakin majalisar dokokin jihar kuma shugaban kwamitin ko-ta-kwana kan yaki da cutar korona ya shaida wa BBC cewa, ganin yadda cutar ta bulla a jihohin da suke makwabtaka da su shi ya sa suka tashi tsaye don shirin ko-ta-kwana.

Ya ce daga cikin matakan da suka dauka, an bai wa jami'an kiwon lafiya horo na musamman, sannan an tanadi wuraren da za a ajiye wadanda suka kamu da cutar idan har ta bulla har waje uku.

Sannan an tanadi kayayyakin kariya daga kamuwa da cutar kamar su takunkumin fuska, da abin wanke hannu da dai makamantansu inji kakakin majalisar dokokin jihar.

Honourable Nasiru Mu'azu Magarya, " Sakamakon dokokin da aka sanya a jihar na hana fita da walwala ga al'ummar jihar, gwamnati ta tanadi abubuwan da za a bawa mutane don a rage musu radadin zaman gida".

Ya ce " Tuni aka fara raba abubuwan da suke saurin lalacewa daga cikin kayayyakin abinci kamar irin kwai wanda aka raba shi a dukkan kananan hukumomin jihar goma sha hudu".

Shugaban kwamitin ko-ta-kwanan ya ce kwan na daga cikin irin gudunmuwar da suka fara samu, kuma nan bada jimawa ba za a fara raba kayan abinci kamar su gero da dawa da shinkafa da sai sauran kayan abinci.

Ya ce da zarar an kammala dukkan shirye-shiryen rabon wadannan kayayyaki za a fara rabawa a dukkan kananan jihohin jihar.

Ya zuwa yanzu dai ba a samu bullar cutar korona a jihar Zamfara ba, amma kuma an samu wadanda suka kamu a makwabciyar jihar wato Katsina inda mutum bakwai suka kamu guda kuma ya rasa ransa.

Adadin mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar korona a Najeriya sun kai 407 kamar yadda hukumar da ke dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta sanar a ranar Laraba da daddare.

Karin bayani kan coronavirus