Najeriya ta gargadi China kan cin zarafin 'yan kasarta

Muhammadu Buhari

Asalin hoton, @BASHIRAHMAAD

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauke tsaurara matakai donmin dakile cutar corona a kasar sa
An wallafa

Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta game da cin mutunci da kyama da 'yan kasarta da wasu bakaken fata 'yan Afirka ke fuska a China.

Ministan harkokin wajen kasar, Geofrey Onyeama, ya ce kasar ba ta ji dadin labarin da ta samu ba kan wariyar da bakake ke fuskanta a kasar a kan cutar korona ba.

A tattaunawarsa da takwaransa na China Zhou Pingjian, ministan ya ce abubuwan da ke faruwa kan bakaken fata a China abin alla-wadai ne.

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni daga China sun nuna cewa daruruwan 'yan Najeriya aka tilastawa barin gidajensu da otel-otel din da suke zaune .

Kuma hakan ya biyo bayan jita-jitar da ake yadawa cewa 'yan Afrika na dauke da cutar korona.

Hotunan bidiyo masu sosa zuciya da aka yi ta yadawa a kafafan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaron China suka rinka cin zarafin bakaken fata.

Wannan dalilin ne a cewar Mista Onyeama, ya sanya Najeriyar jan hankalin China da kuma nuna fushinta da rashin amincewa da wannan keta da ake zargin 'yan kasarta da aikatawa.

Beijing dai ta nuna rashin jin dadinta da wannan batu a cewar Mista Zhou.

Mista Zhou, ya kuma ce China ta dau wannan batu da muhimmanci, domin kasar ba ta manta da gudunmawar da Najeriya ke bata ba musamman a wannan lokaci.

Akwai 'yan Afirka da dama da ke zuwa kasuwanci a China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai 'yan Afirka da dama da ke zuwa kasuwanci a China

Karin Bayani

Tun farkon wannan makon wasu mazauna Guangzhou 'yan Afirka suka ce ana ta korarsu daga gidajensu abin da ya kai ga Amurka ta yi gargadi ga 'yan kasarta bakaken fata su kaurace wa garin.

Wasu rahotanni kuma sun ce ana ta yi wa bakaken fata 'yan Afirka gwajin cutar korona, tare da killace su a gidajensu na tsawon mako biyu duk da cewa ba su nuna wasu alamun cutar ba.

China ce kasar da aka soma samun barkewar cutar korona, sai dai a yanzu kasar ta samu saukin yaduwarta.

Akwai 'yan Afirka da dama a Guangzhou inda ake hada-hadar kasuwanci, wadanda ke zuwa saro kaya zuwa Afrika.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus