Coronavirus: Ministan Tsaron Ivory Coast ya kamu da cutar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Gwajin da aka yi wa Ministan Tsaron Ivory Coast Hamed Bakayoko ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Mr Bakayoko ya ce bai nuna alamomin kamuwa da cutar ba kafin a yi masa gwajin sannan ya bukaci 'yan kasar su dauki matakan kiyaye lafiyarsu.

Tuni dai aka killace ministan.

Ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a Turancin Faransa.

Ya zuwa yanzu Ivory Coast ta tabbatar mutum 323 sun kamu da coronavirus yayin da mutum uku suka warke.

Gwamnati ta sanya dokar hana fita a babban birnin kasar Abidjan sannan ta tilasta wa dukkan 'yan kasar bin dokar hana fita daga karfe 9 na dare zuwa karfe 5 na safe agogon kasar.

A rnar Asabar ne, jami'an lafiyar kasar suka bukaci mutane su rika sanya takunkumin rufe fuska da zummar dakile yaduwar cutar.