Coronavirus: El-Rufai ya kama malamai biyu kan Sallar Juma'a

Nasir El-Rufai

Asalin hoton, @samuelaruwan

Bayanan hoto, An kama malaman biyu ne a Malali da Unguwar Kanawa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu malamai biyu sakamakon bijire wa dokar hana fita da kuma yin taruka a jihar, inda suka gudanar da sallar Juma'a a masallatansu.

Tun a makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta hana sallar Juma'a da addu'o'in coci na ranar Lahadi da sauran taruka, a yunkurinta na dakile yaduwar coronavirus a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, malaman da aka kama sun hada da Malam Aminu Umar Usman da kuma Malam Umar Shangei.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

An kama malaman biyu ne a Malali da Unguwar Kanawa, in ji sanarawar.

Ya bayyana cewa abin da malaman suka yi keta dokar jihar ne da kuma umarnin da manyan malamai suka bayar.

Sanarwar ta kara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu.

Zuwa karfe 4:00 na yammacin Ranar Asabar, mutum 89 ne hukumar NCDC mai yaki da cutuka masu yaduwa ta tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya.

Ga jerin jihohin da cutar ta bulla:

Legas - 59

Abuja - 14

Ogun - 3

Enugu - 2

Ekiti - 1

Oyo - 3

Edo - 2

Bauchi - 2

Osun -1

Rivers -1

Benue - 1

Coronavirsu
Cornavirus