Mutum 20 sun mutu a turmutsutsun karbar taimako a Nijar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

A kalla mutum 20 ne suka rasa rayukansu wasu 12 kuma suka yi rauni yayin wani turmutsutsu wajen amsar taimakon da gwamnan jihar Borno ya kai wa 'yan gudun hijira a jamhuriyar Nijar.

Lamarin ya faru ne da safiyar Litinin inda mutane suka yi dandazo a gidan raya al'adu da wasanni na samari da 'yan mata MJC da ke garin Diffa.

Gidan na cikin wurare biyu da aka kebe domin raba taimakon da gwamnan jihar Bornon Najeriya Umara Zullum ya kai wa 'yan gudun hijirar Najeriyar a kalla su 12,000 da ke zaune a jihar Diffa.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya wallafa hotunansa shi da gwamnan Diffa da na kayan abincin a shafinsa na Twitter.

Shaidun gani da ido sun ce bayan an kwashe yinin farko ana aikin rabon salum-alum, sai a kwana na biyun ne sauran jama'a suka samu labari suka kwararo daga sassan Diffa daban-daban, inda a nan ne wurin ya dinke aka fara turmutsutsu.

Wata majiya ta kusa da asibitin Diffa ta ambato mutum 20 mafiya yawan su mata da yara da kuma tsofafi ne wannan lamari ya rutsa da su.

Yayin da wasu 12 suka yi rauni.

Ba 'yan gudun hijirar ne ba kadai wannan lamari ya shafa, har da 'yan asalin jihar da suka je da zummar samo na sakawa bakin salati su ma sun mutu a turmutsutsun.

Wasu kuwa da yawa kokawa suka yi da yadda mata suka baro gidajensu suka zo amsar wannan taimako da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikin su.

Kawo yanzu dai ba a kai ga bayar da gawarwakin ba ga dangin mamatan, har sai hukumomi sun gama tantancewa kasancewar ba 'yan gudun hijirar Najeriyar ba ne kadai lamarin ya rutsa da su ba.

Gwamnan jihar Diffa tare da rakiyar shugaban majalisar jihar Diffa sun ziyarci asibiti, inda aka kai gawarwakin wadanda suka kwanta dama da kuma wadanda suka jikkata.

Sai dai cikin su ba wanda ya ce uffan game da wannan lamarin.

Sai dai masana al'amuran yau da kullum na ganin faruwar wannan lamari alama ce ta cewa mutanen baki daya na cikin halin rashin abinci.