An karkatar da akalar jiragen saman da ke kan hanyar zuwa Najeriya domin sauka a wasu filayen jiragen sama saboda yanayin hazo da kuma iska da ke kadawa.
A baya-bayan nan ana fuskantar yanayin hazo a Legas da wasu jihohin Najeriya.
Hukumomin kula da filayen jiragen sama sun ce iskar na da karfi sannan tun kwana uku da suka gabata ake juya akalar jiragen da za su sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad zuwa ko dai babban birnin tarayya Abuja ko kuma Accra, babban birnin Ghana.
Ana fuskantar yanayin hunturu da ke kadawa daga yankin Sahara tsakanin Nuwamba zuwa Maris.
Wani matukin jirgin sama ya shaida wa BBC cewa filin jirgin saman Murtala Muhammad ba shi da na'urar da zai taimaka wa jiragen sauka.
Hakan na nufin jiragen ba za su iya sauka ba idan ana hazo.
Dubban fasinjoji ne suka yi cirko-cirko a filin jirgin saman Legas sannan wasu suna wasu filayen jiragen saman domin isa Legas.
Babban jami`in sadarwa na hukumar kula da jiragen sama na Ghana Mr Eric
Mireku Amaning ya fada wa manema labarai cewa, kusan jirage shida ne suka sauya
akala zuwa Ghana mafi yawan su wadanda zasu sauka a Najeriya.
Ya cigaba da cewa jiragen sun hada da
British Airways da Delta Airlines da Emirates Airlines da Air France da Qatar Airways da kuma RwandAir, yayin da wasu daga cikin jiragen har yanzu suke
zaman jiran yanayi ya inganta kafin su tashi zuwa Najeriya.