Shin za a iya cimma muradin samar da kudin bai daya na Eco?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- An wallafa
Bayan shafe tsawon lokaci, kasashen Afirka ta yamma karkashin kungiyar ECOWAS na tattaunawa kan yadda za su samar da kudin bai daya domin amfaninsu.
Tuni wasu daga cikin kasashen a yanzu sun amince su fara amfani da kudin Eco daga shekarar nan ta 2020.
Kwatsam sai ga shi gwamnatin Najeriya ta bukaci a jinkirta kaddamar da kudin na bai daya.
Najeriya ta ce ta bukaci hakan ne saboda akasarin kasashen ba su cika ka'idojin da aka gindaya ba wanda ta ce akwai bukatar a dage lokacin kaddamar da kudin.
A 2019 ne dai Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce ta tsara samar da kudin bai daya na Eco a 2020.
Gwamnatin Najeriy ta ce Togo ce kadai daga yammacin Africa ta cika dukkanin ka'idojin shiga tsarin kudin na bai daya.
Menene kudin eco?

Asalin hoton, Getty Images
Kasashen Afirka ta Yamma guda 15 ne suka amince su fara amfani da kudin na Eco da suka hada da Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Ivory Coast da Mali da Niger.
Sai kuma kasashen Senegal da Togo da Saliyo da Liberia da Nigeria da Gambia da Guinea Conakry da Cape Verde da kuma Ghana.
An dai fara maganar amfani da Eco tun a 2000, sai dai an jinkirta batun tare da yin kwan-gaba-kwan-baya, har sai a shekarar 2019 da Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara ya sanar da matakin kasashe takwas renon Faransa da kuma kasar ta Faransa da suka amince da sauya kudin da suke amfani da shi CFA zuwa ECO.
Sanarwar da aka yi a watan Disambar 2019 ta zo da ba-zata musamman ga wasu kasashen yankunan.
Kasashen na yammacin Afirka 15 sun amince da sunan ECO ne ga a wani taro da suka gudanar a Yunin 2019.
A cewar wani masanin tattalin arziki a Najeriya, kuma tsohon mataimakin gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Ubadia Mailafiya ya ce "Eco kudi ne da gwamnatin Faransa da shugabannin kasashe renon Faransa da ke Afirka ta yamma irinsu Code d'Ivoire da Togo da Mali da Nijar da wasu kasashen suka kulla yarjejeniyar kafa sabon kudi "Eco".
Mailafiya a bayyana cewa kudin Eco zai maye gurbin CFA da a baya kasashen renon yankin Faransa ke amfani da shi.
"Ita Faransa ta dauki nauyin ba da tabbaci na wannan kudin a duniya baki daya."

Dalilin kirkiro kudin
A cewar Mailafiya, an kirkiri kudin domin an dade ana amfani da CFA tun 1945 kuma a Paris ake buga kudin, sannan gwamnatin Faransa ce ta dauki nauyin lura da asusun duka kasashen.
"An duba cewar kasashen ECOWAS suna son su hada kudadensu da na kasashe renon Faransa don a samu kudin bai daya." in ji Mailafiya.
Ya ce an jima kasashen na tattauna hanyoyin da za su cimma wannan tsari saboda "kasashe renon Ingila kamar Najeriya da Ghana da Saliyo da Gambia da Liberia suna tattauna yadda za su kafa nasu kudin."
A watan Disambar 2019 ne, Emmanuel Macron da Alassane Ouattara suka sanar da cewa za su kafa kudin Eco kuma idan sauran kasashen suna da sha'awa za su iya zuwa su hada kai domin samar da kudin.
Daga baya Ghana ta amince cewa za ta shiga cikin gamayyar, amma Najeriya ta ce bata amince ba sannan za ta ci gaba da tattaunawa domin ganin yadda za ta bullowa lamarin.

Alfanun kudin Eco
Kudin Eco yana da matukar alfanu ta bangare da dama, a cewar Farfesa Kabiru Isa Dandago, wani masanin tattalin arziki a Najeriya wanda ke koyarwa a jami'ar Bayeor ta Kano. Ya kuma bayyana ta hanyoyin da za a samu alfanun.
1. Bunkasa cinikayya
Farfesa Dandago ya ce "Wannan tsari ya na da alfanu ga 'yan kasuwa ta kowane bangare, da farko 'yan kasuwar Afirka ta yamma suna da damar shiga kasashen 15 ba tare da sun je ofishin jakadancinsu sun karbi biza ba."
"Idan ma za a yi musu bizar zai zamana biza ce idan aka zo shiga cikin kasar, abin da ake so kawai mutum ya samu shaidar tafiye-tafiye tsakanin kasashen wato fasfo." in ji Farfesa Dandago.
Kudin na Eco kuma zai kawo karshen rashin dai-daiton da ake fama da shi a yankin da kuma ci gaba a fannin tattalin arzikinsu saboda yanzu kasashen Afirka ta yamma za su rika kallon dukkan kasashen ne idan za su samar da kaya domin amfaninsu.

2. Ci gaba ga masu sana'ar canjin kudade
Ga masu sana'ar canjin kudade, su ma hada-hadar cinikayyarsu za ta bunkasa domin za su rika kokarin yin canji tsakanin kudin Eco da sauran kudaden kasashen Turai da sauran kudaden kasashen duniya kamar yadda masanin ya fada.
Hakan a cewarsa, zai sa kasashen Afirka su bunkasa su kuma yi kokarin kamo sauran kasashe da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki.

3. Raguwar hauhawar farashi
Farfesa Dandago ya ce idan har aka samu daidaito a batun kudin na Eco sannan aka fara amfani da kudin yadda ya kamata, hakan zai haifar da raguwar farashin kayayyaki saboda kudin zai saukaka harkokin kasuwanci ta fuskoki da dama.
Gwamnatocin kasashen ba za su samu damar yin amfani da hauhawar farashin kayayyaki ba wajen cike gibin da aka samu a kasafin kudinsu.

4. Fatara da talauci za su yi kasa
Tsarin kudin na Eco zai taimaka wa kasashen da ba su da arziki kamar Saliyo wadda ake kallo a matsayin karamar kasa da ka dogara kan wasu kasashen wajen samun abinci.

5. Samar da ayyukan yi
Hada-hadar cinikayyar da za a yi za ta taimaka wajen samar wa da mutane ayyukan yi wanda zai taimaka musu su tsaya da kafarsu saboda tsarin zai samar da karuwar kasuwanci ga 'yan kasuwa tare da bada damar fitar da kayayyaki tsakanin kasashen.
Ya ce samun wannan zai sa dan kasuwa ya shiga a dama da shi a kasashen saboda ana sa ran "kudin zai samu wata cibiya daya kamar babban banki wanda zai rika ba da kudaden ga bankuna da suke kasashen 15, kuma a rika bayar wa ga 'yan kasuwa domin cinikayya."

6. Samar da hadin kai
A cewar malami a sashen tattalin arziki a jami'ar gwamnatin tarayya, Kashere a jihar Gombe, Dr Mustapha Kabara ya ce "kasashen na yammacin Afirka za su zama suna magana da murya daya ta yadda duk wata barazanar tattalin arziki da ga kasashen da basa cikin tsarin kamar kasashen Turai da Amurka ta tunkari.
Zai kasance ba komai kasashen yamma za su gabatar wa kasashen yammacin Afirka zai samu karbuwa ba saboda suna da hadin kai da tsarin tattalin arziki sannan kuma suna magana da murya daya.

Sai dai duk abin da yake da alfanu yana da akasinsa kuma masana na ganin akwai kalubale idan har aka fara amfani da wannan kudin na bai daya tsakanin kasashen yankin.
Kasashen za su rasa ikon da suke da shi kan kasashensu musamman ta bangaren tattalin arziki kamar fito da kayyade adadin kudin ruwa.
Duk da kananan kasashe za su samu habaka a tattalin arzikinsu, alfanun tsarin zai fi yin tasiri kan kasashen da suke da karfin tattalin arziki.
Sai kuma banbancin harshe tsakanin kasashe renon Ingila da Faransa na iya shafar zirga-zirgar ma'aikata sannan kuma zai iya ta'azzara matsalar rashin ayyukan yi musamman a kasashen da suke da karamin karfi.

Ra'ayin wasu al'umar kasar
Wani mai sana'ar canjin kudade a Najeriya Abdulhadi Rabiu Kura ya ce "tsarin ci gaba ne saboda mutum zai dauki kudi zuwa kasashen ba tare da fargabar samun canji ba."
Ya kara da cewa matakin zai sa kudin ya yi karfi har kasashen duniya su rika mu'amala da kudin.
A cewarsa "abin dubawa shi ne da kasashen Turai suka yi irin wannan tsari har suka samar da Euro wane irin ci gaba aka ga an samu a tattare da su."
Ya ce Ingila ta yi hikima saboda "bata yadda ta soke kudinta kamar yadda Jamus da Italia suka soke nasu."
Ya yi fatan Najeriya ma ba zata soke nata kudin ba "ta yi irin na Ingila don ganin yadda tsarin zai kasance."
Ita ma Jamila da ga Ghana cewa ta yi tsarin kudin na Eco zai taimaka wa 'yan kasashen da suke kasuwanci su gudanar da kasuwancinsu ba tare da wata fargaba ba.
"Idan ka yi tafiya kaje wani gari ba sai ka canja kudi don yin ciniki ba" in ji ta.
Shi kuwa Abdulbasit Ibrahim a Abuja, babban birnin Najeriya yana ganin "ba za a samu wani alfanu ba daga tsarin saboda akasarin kayayyakin da sukesamar da ci gaba na karkashin ikon kasuwannin duniya."
Ya kara da cewa tsarin kamar wani abu ne da dauke hankali amma idan shugabannin suka yi abin da ya kamata, tsarin zai kawo karshen hau-hawar farashin kaya."
Makomar Eco
Ubadia Mailafiya ya ce tun a baya kasashen Faransa na Afirka ta yamma suna amfani da CFA kuma abin ya kara karfafa tattalin arzikinsu - ya sa kudinsu yana da dan karfi a sha'anin kasuwancin duniya baki daya."
A ganinsa, idan har aka sasanta da kyau, kudin na Eco ya na iya taimakawa wajen karfafa tattalin arzikin kasashen da za su yi amfani da kudin.
Sai dai ya ce abin damuwar shi ne yadda aka zo aka kafa kudin ba tare da an sasanta da Najeriya da sauran kasashen renon Ingila ba wanda masanin ya ce zai iya kawo cikas.
'Faransa ta ce ta ba da tabbaci kan kudin na Eco, sai dai bamu san ko Najeriya za ta amince ko ba za ta amince ba."
Ya ce idan har aka bi sha'anin da kyau kuma har Najeriya da sauran kasashe renon Ingila a yankin Afirka ta yamma suka amince, za su iya hada kai da sauran kasashe renon Faransa har a samar da Eco.
Ya ce yin hakan zai taimaka sosai a sha'anin kasuwanci da karfafuwar tattalin arziki.
"Amma sai an bi abin a hankali, an samu ra'ayin kowa da kowa kuma kowa ya amince da abin da ya kamata a yi da matakai da ya kamata a duka domin a samu ci gaba a Afirka ta yamma gaba daya." in ji Mailafiya.











