Wasu kasashen Afirka sun ki yarda a sauya CFA zuwa ECO

Asalin hoton, Getty Images
Wasu kasashen Afirka da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka sun nuna adawa da matakin sauya sunan kudin CFA ta Faransa zuwa ECO wanda kasashen za su rika amfani da shi.
Kasashen da suka hada da Guinea sun ce shugaban Ivory Coast Allassane Outtarra kuma shugaban ECOWAS ya dauki matakin ne ba tare da tuntubar sauran mambobin kingiyar ba.
Yayin wani taron Ministocin kudi da Gwamnonin Babban Banki na kasashen yammacin Afrika a Abuja, mambobin kasashen sun kara jaddada matsayin na kin amincewa da kudin na Eco, inda suka ce Shugaba Outtarra, bai tuntube su ba kafin zartar da wannan matsayi.
Kasashe 8 na yammaci da tsakiyar Afirka ne ke amfani da kudin CFA na Faransa, wadanda yawancinsu Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
A makon jiya ne shugaban Ivory Coast Allassan Ouattara ya sanar da cewa za a sauya kudin CFA zuwa ECO, amma babu tabbas kan yadda wannan yunkuri zai yi tasiri tsakanin mambobin kasashen na ECOWAS don samar da kudin ba-daya wanda ake kira ECO.
Tsarin kudin na bai-daya dai na nufin mambobin ECOWAS 15 za su mayar da harakokin sha'anin kudinsu ga kungiyar, wani matakin da ake ganin da wuya ya iya cimma nasara.
Kuma batun cewa kudin Yuro na Turai ne zai kasance a matsayin ma'aunin sabon kudin na ECO, zai kara haifar da cikas ga cimma burin wasu kasashen na tabbatuwar bukatarsu.






