Gari 'mafi gaskiya' a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da al'ummar birnin Tokyo babban birnin kasar Japan ke kai wa kusan milyan 14, miliyoyin abubuwa suke bata a kowace shekara amma mafi yawansu suna komawa ga masu su, abin da ya sa ake ganin Japan din ce kasa "mafi gaskiya" a duniya.
A shekarar 2018 kadai 'yan sanda a Tokyo sun mayar da katin shaida (ID Card) 545,000 ga masu su - kashi 73 cikin 100 kenan na katinan da suka bata.
Kazalika, wayoyin salula guda 130,000 (kashi 83% kenan) da lalita (wallet) 240,000 (65%) aka mayar kuma mafi yawan lokaci ana mayar da su a ranar da aka yar da su.
Cikin wayar salula 156,000 da aka kai wa 'yan sanda a 2018 ba a taba bai wa wanda ya tsinta abin da ya tsinta din ba, 'yan sanda ma ba su rike ko daya ba.
Kashi 17% da ba a iya gano masu su ba lalata su kawai aka yi.
"Lokacin da nake San Francisco a Amurka na ji labarin wani ya yar da lalitarsa a garin Chinatown sai wanda ya tsinta ya kai wa 'yan sanda," in ji Kazuko Behrens, wani masanin halayyar dan Adam.
Saboda ba a saba ganin haka ba a yankin sai aka yi ta yabonsa har ma aka yi hira da shi a labarai ana ce masa "mai gaskiya".
Sai dai irin wannan gaskiyar ba wani abin mamaki bane a yankin Behren na Japan.
"A Japan sai dai ka ji ana cewa, 'Yauwa, ai da ma na san za su dawo shi." Hasali ma abin al'ajabi ne idan mutum ya tsinci jakar aljihu bai kai wa 'yan sanda ba. Za a sha mamaki kwarai.
Sunan 'yan sandan unguwar kōban sun fita daban da sauran 'yan sanda a duniya. Suna nan da yawa a Tokyo - akwai 'yan sanda 97 a duk murabba'in kilomita 100 - a Landan 11 ne kacal a wannan ma'aunin.
A Tokyo dai ba za ka taba rasa agaji ba daga 'yan sanda a duk inda kake.
An san 'yan sandan da yi wa matasa masu kiriniya tsawa da kuma taimaka wa tsofaffi wurin tsallaka titi.
"Idan yara suka gan su ('yan sanda) a titi sukan gaishe su," in ji Masahiro Tamura, wani farfesa a bangaren shari'a a Jami'ar Kyoto Sangyo ta Japan.
"Sukan ('yan sandan) kwankwasa wa tsofaffin kofa domin su tabbata suna cikin koshin lafiya."











